Labari Mai Daɗi: Gwamnan APC Ya Tausaya Wa Talakawa, Ya Ɗauki Muhimman Matakan da Za a Samu Sauƙi

Labari Mai Daɗi: Gwamnan APC Ya Tausaya Wa Talakawa, Ya Ɗauki Muhimman Matakan da Za a Samu Sauƙi

  • Babajide Sanwo-Olu ya sanar da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin rage wa mazauna jihar Legas raɗaɗin halin matsin da aka shiga
  • Gwamnan ya bayyana rage wa ma'aikata ranakun aiki daga kwanaki 5 zuwa 3, yayin da malamai kuma za a ba su alawus na hawa mota
  • Bayan haka gwamnan ya faɗi wasu matakan waɗanda suka haɗa da rage wani kaso na kuɗin sufurin motocin gwamnati a jihar Legas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya sauƙaƙa wa ma'aikatan gwamnati kan zuwa wurin aiki bisa la'akari da halin tsadar rayuwa da ake ciki.

Gwamnan na jam'iyyar APC ya sanar da cewa ma'aikatan gwamnati daga mataki na 1-14 zasu fara zuwa wurin aiki na kwanaki uku a kowane mako.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Farashin dala zai faɗi warwas a Najeriya nan ba da daɗewa ba, gwamna ya magantu

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnan Legas Ya Sanar da Rage Ranakun Aikin Ma'aikata Zuwa Kwana 3 a Mako Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Getty Images

Ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne a wani ɓangare na kokarin rage wa mutane raɗaɗin matsin tattalin arzikin da aka shiga a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanwo-Olu ya sanar da wannan garaɓasa ne a wurin tattaunawa da ƴan jarida kai tsaye mai take, "Sanwo-Olu ke magana," kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sai dai ya ce ma'aikata a ɓangaren koyo da koyarwa watau malamai zasu ci gaba da zuwa aiki sau biyar a mako amma gwamnatinsa za ta samar musu alawus na kuɗin mota.

A rahoton Channels tv, Gwamnan ya ce:

"Zamu fara da ma'aikatan gwamnati daga mako mai zuwa, kananun ma'aikata zasu koma zuwa aiki sau uku a mako, su kuma ma'aikatan matakai na 15-17 zasu fito aiki sau huɗu a mako."

Wane mataki ya ɗauka don sauke farashin abinci?

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4

Dangane da tashin farashin abinci, ya kara da cewa gwamnatinsa za ta bude wasu kasuwannin da ‘yan Legas za su iya siyan kayan abinci a farashi mai rahusa.

Ya kuma ƙara da cewa daga ƙarshen makon nan za a fara ragin kaso 25% na kuɗin sufuri a motocin kamfanonin sufuri na gwamnatin jihar Legas.

Wane mataki gwamnati ke ɗauka kan wahalar da ake ciki?

A wani rahoton kuma Kashim Shettima, mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

A cewar mataimakin shugaban ƙasan, cire tallafin man fetur ya sa shafaffu da mai suka riƙa kawo cikas, amma ya yi amanna cewa cewa ƙasar nan na kan turbar dawowa daidai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel