Mataimakin Shugaba Tinubu da Gwamnoni 3 Sun Halarci Jana'izar Gwamnan APC da Ya Mutu a Owo

Mataimakin Shugaba Tinubu da Gwamnoni 3 Sun Halarci Jana'izar Gwamnan APC da Ya Mutu a Owo

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima da shugaban APC na ƙasa sun halarci bikin janazar tsohon gwamnan Ondo a cocin Owo
  • Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu da Dapo Abiodun na jihar Ogun na cikin manyan mutanen da aka gani a wurin jana'izar marigayin
  • Rahotanni sun nuna cewa tun ranar Litinin aka fara bukukuwan binne marigayi Akeredolu kuma a yau ne ake sa ran za a binne shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Rahotanni sun nuna cewa tuni aka fara jana'izar tsohon gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, a cocin St. Andrews da ke layin Imola a Owo a jihar Ondo.

Marigayi Akeredolu ya mutu ne ranar Laraba 27 ga watan Disamba, 2023 yana da shekaru 67 a duniya, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Edo: Bayan matsalar da aka samu, APC ta bayyana wanda ya lashe tikitin takarar gwamna

Marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.
Mataimakin Shugaba Tinubu da Gwamnoni 3 Sun Halarci Jana'izar Gwamnan APC da Ya Mutu Hoto: Oluwarotimi Akeredolu
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya cika ne a asibitin kasar Jamus bayan fama da cutar kansa ta tsawon lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun ranar Litinin aka fara bukukuwan jana'izar marigayi tsohon gwamnan kuma haka aka ci gaba da harkokin tsawon wannan mako.

Manyan kusoshin da suka halarci jana'izar Akeredolu

Fitattun ƴan Najeriya da suka halarci jana'izar sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima da gwamnan Ondo mai ci, Honorabul Lucky Aiyedatiwa.

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Dakta Abdullahi Ganduje, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun sun halarci wurin.

Jaridar Punch ta tattaro cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya halarci wurin jana'izar da ƙarin wasu manyan mutane.

A tsare-tsaren da aka yi na jana'izar, za a binne marigayin a wata maƙabarta dake garin kuma dangin Akeredolu ne kawai za su halarta.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimami yayin da a yau za a binne tsohon gwamnan APC a kauyensu, bayanai sun fito

APC ta bayyana ɗan takararta a zaben gwamnan jihar Edo

A wani rahoton kun ji cewa Jam'iyyar APC ta ayyana Sanatan Edo ta Tsakiya, Monday Okpebholo, a matsayin ɗan takararta a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa a 2024

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani, Gwamna Bassey Otu, ya bayyana Okpebholo a matsayin wanda ya samu nasara da ƙuri'u 12,433

Asali: Legit.ng

Online view pixel