Shugaban Majalisar Dattawa Ya Tona Asirin Masu Ɗaukar Nauyin Zanga-Zanga Kan Tsadar Rayuwa

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Tona Asirin Masu Ɗaukar Nauyin Zanga-Zanga Kan Tsadar Rayuwa

  • Sanata Godswill Akpabio ya yi zargin cewa akwai wasu tsiraru a gefe da ke ɗaukar nauyin masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa
  • Shugaban majalisar dattawan ya ce mafi akasarin mutanen da ake amfani da su wajen zanga-zangar ba su san kokarin da FG ke yi ba
  • Akpabio ya jaddada cewa majalisar dokokin ƙasar nan ba zata amince da duk wani abu da ba zai amfani ƴan Najeriya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya yi iƙirarin cewa wasu ne suka kitsa tare ɗaukar nauyin zanga-zangar da mutane ke yi kan tsadar rayuwa.

Jaridar The Cable ta tattaro cewa mutane sun fito zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar nan, ta baya-bayan nan ita ce wadda aka yi Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Akpabio ya samu matsala da 'yan Najeriya kan abu 1 tak

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Akpabio: Zanga-Zangar da Aka Yi Kan Tsadar Rayuwa Ɗaukar Nauyinta Aka Yi Hoto: Sanata Godswill Akpabio
Asali: Facebook

Mazauna sun bazama kan tituna a jihohin Kano, Neja da Sakkwato domin nuna fushinsu kan halin matsin tattalin arziki da yunwar da ake ciki, rahoton Daily Trsut.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hauhawar farashi dai na ta kara karuwa a Najeriya tun bayan da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya kawo karshen tallafin man fetur da kuma hada kan farashin canji a 2023.

Su wa suka kitsa zanga-zangar da ake yi a jihohi?

Da yake jawabi a zauren majalisar dattawa a ranar Talata, Sanata Akpabio ya ce masu zanga-zangar ba su da masaniya kan kokarin da gwamnati da majalisar ke yi domin magance matsalar.

Akpabio ya ce

"Kuna ganin yadda ake ta zanga-zanga a nan da can waɗanda wasu tsiraru suka ɗauki nauyi amma mutanen da suka fito zanga-zangar ba su san komai ba.
"Mafi akasarin waɗanda aka ɗauki nauyi suka fito zanga-zanga ba su san faɗi tashin da majalisar dattawa da gwamnatin tarayya ke yi domin daƙile lamarin ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun toshe fitaccen titi a Arewacin Najeriya, sun sace matafiya masu ɗumbin Yawa

"Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce gwamnatocin jihohi sun samu ƙarin Naira biliyan 30 a ƴan watannin nan daga hukumar tattara haraji (FIRS) baya ga kasafinsu na wata-wata.
"An ƙara musu kuɗin ne domin magance karancin abinci. Saboda haka muna fatan jihohi zasu yi amfani da waɗannan kudi wajen tabbatar da wadatar abinci."

Shugaban majalisar dattawan ya ce majalisar dokokin kasar ba za ta amince da duk wani abu da ba zai amfani ‘yan kasa ba.

Tsohon gwamnan Kwara na hannun EFCC

A wani rahoton kuma Jami'an hukumar EFCC sun ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed a ofishin da ke Ilorin

Bayanai sun nuna cewa hukumar ta gayyaci Ahamed domin ya amsa tambayoyi kan zargin karkatar da wasu kudi N10bn a lokacin mulkinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel