Za a Ƙara Yawan Jihohin Najeriya Daga 36 Su Koma 42? Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fayyace Gaskiya

Za a Ƙara Yawan Jihohin Najeriya Daga 36 Su Koma 42? Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fayyace Gaskiya

  • Benjamin Kalu, mataimakin shugaban majalisar wakilai ya yi ƙarin haske kan shirin ƙara yawan jihohi zuwa 42 a Najeriya
  • Ɗan majalisar ya ce har yanzu kwamitin gyaran kundin tsarin mulki bai samu takarda kan kirƙiro karin jihohi 6 a ƙasar nan ba
  • A cewarsa, zasu yi aiki tsawon watanni 24 kuma sun shirya tsaf domin cika muradan ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kalu, ya ce babu wata takardar kara yawan jihohi zuwa 42 a gaban kwamitin yi wa kundin tsarin mulki garambawul.

Sai dai ya ce majalisar ta shirya tsaf domin ganin an biya bukatun ‘yan Najeriya ta hanyar gyara kundin tsarin mulkin kasa wanda zai dauki tsawon watanni 24.

Kara karanta wannan

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin tarayya saboda abu 1, bidiyo ya bayyana

Benjamin Kalu.
"Babu wata takarda kan kara yawan jihohi zuwa 42 a Najeriya in ji Kalu Hoto: Benjamin Kalu
Asali: Facebook

Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Siyasa a Yau na Channels tv ranar Litinin, 27 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin kaddamar da kwamitin jiya a Abuja, kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya bukaci su yi aiki a kan manufofin majalisar tare da sake duba kudirin baiwa mata kujeru a majalisar.

Shin za a kirkiro karin jihohi 6 a Najeriya?

Da aka tambaye shi ko akwai shirin samar da karin jihohi shida, Kalu ya ce:

"Ba mu samu wata sanarwa ba dangane da hakan (ƙara yawan jihohi zuwa 42), amma, idan abin da ’yan Najeriya ke so kenan, za mu yi.
"A koda yaushe mu tuna cewa daidaito, adalci, da daidaitawa sun zama dole ga dukkan shiyyoyi 6 da muke da su a ƙasar nan. Don haka duk wanda ya zo da buƙata ba zamu jefar ba."

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsaida lokacin da za a fito da sabon kundin tsarin ms`ulki a Najeriya

Za a kafa dokar samar da ƴan sandan jihohi

Mataimakin shugaban majalisar ya kuma ce Najeriya ta ƙagara ta samu dokar da za ta goyi bayan samar da ‘yan sandan jihohi, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewarsa, halin rashin tsaron da ake ciki a sassan ƙasar nan ya kai matakin da ba zai yiwu a masa rikon sakainar kashi ba.

Har ila yau, Kalu ya ce zasu kammala duk wani gyara su shirya cikakken kundin tsarin mulki domin shugaban kasa ya rattaɓa hannu a cikin watanni 24 masu zuwa.

An ƙara maka Gwamna Fubara da majalisa a kotu?

A wani rahoton kuma Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula sun kai ƙarar Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da majalisar dokokin jihar gaban kotu.

Ƙungiyoyin sun kai ƙarar ɓangarori biyu na gwamnati gaban kotu ne kan sauya sheƙar ƴan majalisar jiha 27 daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262