Dan Takarar Shugaban Ƙasa, Obi Na Shirin Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar Adawa? Gaskiya Ta Bayyana

Dan Takarar Shugaban Ƙasa, Obi Na Shirin Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar Adawa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Peter Obi ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin tattara kayansa ya fice daga Labour Party (LP) saboda rikicin da ya dabaibayeta
  • Tawagar midiya ta tsohon gwamnan 'Peter Obi Media Reach (POMR)' ta ce rahoton ƙanzon kurege ne kuma wasu bara gurbi ne suka kirkire shi
  • Hadimin Obi na midiya, Michael Jude Nwolisa, ya ce Obi na nan daram a jam'iyyar LP kuma babu abinda ya sauya daga yadda ya sadaukar da kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya yi martani kan jita-jitar yana shirin sauya sheka daga LP.

Wani rahoto da ake yaɗawa ya yi ikirarin cewa Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya gama tsara barin jam'iyyar LP yayin da rikicin cikin gida ya mata katutu.

Kara karanta wannan

Atiku ya tsufa ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben 2027? An fayyace gaskiya

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.
Peter Obi Ya Yi Magana Kan Yiwuwsr Ficewa Daga Laboir Party Saboda Rikici Hoto: Mr Peter Obi
Asali: Facebook

A cewar rahoton jaridar Vanguard, Obi ya yi watsi da rade-radin, yana mai bayyana hakan a matsayin aikin wasu bara gurbi masu aikata barna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi na shirin sauya sheƙa daga LP?

Mai taimakawa kan harkokin midiya na Peter Obi Media Reach (POMR), Michael Jude Nwolisa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu.

Ya ce:

"Ku yi watsi da labarin ƙarya kuma mara tushe da ake yaɗawa cewa yana shirin raba gari da jam'iyyar LP, ko kaɗan ba gaskiya bane.
"Labarin bai da tushe daga Peter Obi ko tafiyar Obidient amma wasu bara gurbi da ke kokarin yaɗa ɓarna ne suka shirya shi domin tarwatsa jam'iyyar LP."

Meke faruwa a Labour Party?

Nwolisa ya bayyana cewa dukkan masu hannu a haddasa rikicin cikin gida a LP maƙiyan demokuraɗiyya ne.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Yadda Buhari ya tura DSS don su kashe ni, Sunday Igboho ya yi zargi

Ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Anambra na nan daram a matsayin cikakken mamban LP kuma ba shi da wani yunƙuri na raba gari da fitacciyar jam'iyyar.

"Saboda haka Peter Obi na farin cikin tabbatar wa ƴan Najeriya da ƴan Obidient cewa yana nan daram ba kuma kokarinsa na ceto Najeriya daga miyagu ba zai tsaya ba."

Shettima da Ganduje sun je coci wurin jana'iza

A wani rahoton kuma Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima da shugaban APC na ƙasa sun halarci bikin janazar tsohon gwamnan Ondo a cocin Owo.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu da Dapo Abiodun na jihar Ogun na cikin manyan mutanen da aka gani a wurin jana'izar marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262