Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Bayyana Yadda Manufofin Tinubu Suka Jawo Wahala a Najeriya

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Bayyana Yadda Manufofin Tinubu Suka Jawo Wahala a Najeriya

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fuskanci suka sosai sakamakon halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya caccaki manufofin tattalin arziƙi na Tinubu, inda ya ce nasarorin da aka samu ba su da yawa idan aka kwatanta da raɗaɗin da ake ciki
  • Adebayo ya ce ƴan Najeriya za su kasance tare da munanan manufofin Tinubu na tsawon shekaru huɗu masu zuwa bayan cire tallafin man fetur da karya Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Adewole Adebayo, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP a zaɓen 2023, ya ce ƴan Najeriya za su kasance da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manufofinsa "marasa kyau" na tsawon shekaru huɗu.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya yi sabuwar fallasa kan adadin man fetur din da ake sacewa a Najeriya

Adebayo ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, yayin da yake magana kan wahalhalun da ake ciki a Najeriya a shirin 'Sunday Politics' na gidan talabijin na Channels tv.

Adebayo ya soki manufofin Tinubu
Adebayo ya ce manufofin Tinubu ba su da kyau Hoto: Adewole Adebayo, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Me yasa Adebayo ya soki manufofin Tinubu?

A cewar mai fatan zama shugaban ƙasar, idan da shi ne ba zai yi cire tallafin man fetur a ranar da ya zama shugaban ƙasa ba, amma da ya yi gyaran dokar kasafin kuɗi na 2023 don ba da damar ci gaba da tallafin na wani lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana game da manufofin Bola Tinubu, ɗan takarar na jam’iyyar SDP ya ce:

“Waɗannan manufofin ba su da kyau, ba don jam’iyyar da ke sanar da su ba amma don ba su dace da mu ba.

Adebayo ya ƙara da cewa nasarorin da aka samu a manufofin ba su kai raɗaɗin da ake sha saboda su ba.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

Manufofin Tinubu ba su haifar da ɗa mai ido ba

Ya yi nuni da cewa, ya kamata gwamnatin Tinubu ta kasance “ta rage girman kai” don yin abin da ya dace don samar da sauƙi ga ƴan Nijeriya.

A kalamansa:

"Mutanen Najeriya sun zaɓi waɗannan manufofin, ba manufofi ba ne masu kyau amma har zuwa zaɓe na gaba, kuna nan tare da waɗannan manufofin.

Atiku Ya Ci Gyaran Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya yi wa Shugaba Tinubu gyara kan yadda ake gudanar da mulki.

Ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya buƙaci Tinubu da ya yi koyi da takwaransa na ƙasar Argentina, domin tsamo ƙasar nan daga halin da take ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel