Tsohon Gwamnan Arewa Ya Shiga Babbar Matsala, An Fara Bincike Kan Makudan Kuɗi Na Shekaru 8

Tsohon Gwamnan Arewa Ya Shiga Babbar Matsala, An Fara Bincike Kan Makudan Kuɗi Na Shekaru 8

  • Gwamna Hyacinth Alia ya fara binciken tsohon gwamnan jihar Benuwai da ya sauka, Samuel Ortom, kan yadda aka kashe dukiyar jihar a shekara 8
  • Ƴa kafa kwamitin bincike guda biyu da zasu yi aikin gano yawan kuɗin da aka samu da yadda aka kashe su, da kuma yadda aka siyar da kadarori
  • Da yake jawabi, Gwamna Alia ya ce ba shi da wata ɓoyayyar manufa kan wannan binciken illa tabbatar da al'umma sun amfana da kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benuwe, Hyacinth Alia, ya fara binciken tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom, kan yadda aka kashe kuɗin gwamnati a mulkinsa.

Gwamna Alia ya fara bin ba'asain yawan kuɗin da suka shiga baitul malin jihar Benuwai da kuma yadda aka kashe su a mulkin Ortom daga 2015 zuwa watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Samuel Ortom da Gwamna Alia.
Gwamna Ortom Ya Fara Shirin Bincikar Tsohon Gwamnan Benue, Ortom Hoto: Samuel Ortom, Hyacinth Alia
Asali: Twitter

A wani ɓangare na binciken, Alia ya kafa kwamitocin bincike guda biyu da zasu gano kuɗin shiga da kuma yadda aka ɓatar da su kama daga bada kwangiloli da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alia ya kaddamar da kwamitocin a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar Benuwai da ke Makurɗi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wane abubuwa za a bincine Ortom a kansu?

Gwamna Alia ya umurci kwamitin bincike kan sayar da kadarorin gwamnati da ya binciki duk yarjejeniyoyin da aka kulla tare da bayar da shawarwarin da suka dace kan matakin da za a ɗauka na gaba.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta da wata manufa game da binciken sai dai "bukatar tabbatar da cewa jihar Binuwai ta samu moriyar duk wani abu da aka samu a gwamnatin da ta gabata."

Kwamitocin biyu za su tafiyar da harkokin aikin da gwamnan ya rataya musu ne karkashin jagorancin mai shari'a Taiwo Taiwo da mai shari'a Paul Appolos.

Kara karanta wannan

Dandutse: Ƴan bindiga sun kashe babban soja da wasu jami'ai biyu, sun tafka ɓarna kan bayin Allah

An buƙaci su bincike adadin kuɗin da gwamnatin jihar ta samu da kuma yadda aka kashe su a tsawon shekaru takwas da Ortom ya yi a madafun iko, Vanguard ta rahoto.

Da yake jawabi mai shari'a Taiwo Taiwo wanda ke jagorantar kwamitin binciken kudaden shiga da yadda aka kashe su, ya ce tawagarsa za ta yi aiki ne domin amfanin jihar.

Ortom ya gama shirin sauya sheƙa zuwa APC?

A wani rahoton kuma Samuel Ortom ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya kammala shirin sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Tsohon gwamnan jihar Benuwai kuma mamban G5 ya ƙara jaddada cewa yana nan a inuwar babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel