Tsohon Gwamnan Arewa Ya Gama Shirin Ficewa Daga PDP Zuwa APC? Gaskiya Ta Yi Halinta

Tsohon Gwamnan Arewa Ya Gama Shirin Ficewa Daga PDP Zuwa APC? Gaskiya Ta Yi Halinta

  • Samuel Ortom ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya kammala shirin sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Tsohon gwamnan jihar Benuwai kuma mamban G5 ya ƙara jaddada cewa yana nan a inuwar babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP
  • Ya bukaci mambobin PDP a jihar su aje komai a gefa, su dawo a haɗa kai domin farfaɗo da martabar jam'iyyar a babban zaɓe na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).

Mista Ortom ya musanta raɗe-raɗin ne yayin da yake jawabi a wurin taron shugabannin PDP na jihar da aka faɗaɗa ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Atiku ya tsufa ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben 2027? An fayyace gaskiya

Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom.
Ina nan daram a matsayin mamban PDP, in ji tsohon gwamnan Benue Hoto: Samuel Ortom
Asali: Facebook

Haka nan kuma a jawabinsa, tsohon gwamnan ya jaddada cewa yana nan daram a jam'iyyar People Democratic Party (PDP), kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ortom ya kuma bayyana bukatar da ke akwai na mambobin PDP a jihar Benuwai su haɗa kansu wuri guda, domin farfaɗowa daga kayen da suka sha a babban zaɓen 2023.

A rahoton Leadership, tsohon gwamnan ya ce:

"A yanzu bamu bukatar mu tsaya kwaƙuo laifin waye, zaɓe dai ya zo kuma ya wuce, saboda haka dole nu shata layi, mu tunkari gaba. PDP ce jam'iyya daya tilo da ke da karfi da karbuwa a zuƙatan jama'a.
"Idan muka sake sadaukar da kanmu, zamu sake farfaɗo da jam'iyyar mu gobe, za mu yi nasara a zabe mai zuwa. Babu wani saɓani tsakanina da Moro da Suswam.

Tsohon gwamnan zai koma APC?

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban ƙasa, Obi na shirin sauya sheƙa daga jam'iyyar adawa? Gaskiya ta bayyana

Mista Ortom ya bayyana cewa jita-jitar cewa zai sauya sheka zuwa APC ba gaskiya bane domin shi ne jagoran PDP a jihar Benuwai.

Ya ci gaba da cewa:

"Jita-jitar da ake wai zan koma APC ba ta da tushe duba da ni ne jagoran PDP na jihar nan wanda kuma ba karamin nauyi bane, ba zan bar PDP zuwa kowace jam'iyya ba.
"APC ba ta gayyace ni zuwa cikinta ba, ni ba mai tsalle-tsalle ba ne da zan rika tafiya daga wannan wuri zuwa wancan, na tsayu a jam’iyyata (PDP)."

Me ya kamata PDP ta gyara kafin 2027?

Sani Adamu, wani jigon PDP a jihar Katsina ya shaida wa Legit Huasa cewa ya kamata jam'iyyar ta sake karatu a natse idan tana son farfaɗowa a zaɓe na gaba.

A cewarsa, tsofaffin gwamnoni irinsu Ortom, Ibrahim Shehu Shema na jihar Katsina ba abin yardar wa bane kuma su ma bai kamata suna yin wasu abubuwan ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya ƙara haddasa sabuwar rigima a jam'iyyar PDP kan muhimmin abu 1

Ya ce:

"Ina ganin PDP na da wata dama a hannunta na kwace mulkin ƙasar nan daga hannun APC a 2027 saboda mutane na shan baƙar wahala, idan har muka tsaida wanda ya dace kuma muka haɗa kan mu za a samu nasara.
"A zaben da ya wuce mun ga illar rabuwar kai domin ba don haka ba Obi da Atiku duk ƴan. PDP ne, amma sai APC ta yi amfani da rikicin mu ta sake samun nasara, lokaci ya yi da zamu farka."

Wane gwamnan PDP ne aka kai ƙara kotu?

A wani rahoton kun ji cewa Fararen hula sun gurfanar da Gwamna Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas a gaban babbar kotun tarayya kan sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Enefa Georgewill, ya ce sun nemi kotun ta ayyana kujerun ƴan majalisa 27 a matsayin babu kowa

Asali: Legit.ng

Online view pixel