Siyasar Najeriya
Sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP (BoT), Ahmed Makarfi, ya yi murabus daga kan mukaminsa. Ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai yi murabus.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi gargadi kan yawan sauya shekar da wasu 'yan siyasa suke yi zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, Rt. Hon. Kizito Bonzena ya jagoranci yam Majalisa 15 ciki har da mataimakinsa sun fice daga PDP zuwa APC.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa taron PDP da aka gudanar a jihar Oyo ba komai ba ne face taron nishadi.
Dan marigayi tsohon shugaban kasa, Johnson Aguiyi-Ironsi, Thomas Aguiyi-Ironsi ya ce ya bar komai ga Allah bayan kashe mahaifinsa, ya ce Najeriya ta koyi darasi.
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya kwatanta jam’iyyar APC da jirgin Annabi Nuhu, yana cewa ita ce kadai hanyar ceto Najeriya, lamarin da ya jawo martani masu zafi.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, da Shugaban APC na kasa, Prof. Nentawe Yilwatda, sun karɓi daruruwan masu sauya sheƙa daga jam’iyyu biyar zuwa APC a Plateau.
PDP ta rushe dukkan tsarin jam’iyya a Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Rivers yayin babban taron zabe a Ibadan, tana mai cewa yanayin siyasa ne ya tilasta hakan.
Mataimakin Shugaban APC na Kudu maso Gabas, Ijeoma Arodiogbu ya ce ba zai taba yiwuwa ba Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wata kawance da Atiku Abubakar.
Siyasar Najeriya
Samu kari