Siyasar Kano
Sanata Barau Jibrin ya karbi wasu 'yan NNPP zuwa APC daga Kano ta Arewa a majalisar dattawa. 'Yan NNPP sun ce sun koma APC ne saboda rikicin Kwankwasiyya.
Wata kungiyar Kwankwasiyya ta yi kira ga Abba Kabir Yusuf kan rika damawa da wadanda suka sha wahala a zaben 2023. Ta ce wasu na neman kudi ne a gwamnati.
Rt. Hon. Alhassan Doguwa ya ce ba sa jin tsoron kowa ya shiga APC, yana mai jaddada cewa Kano da Najeriya duk tafiyar Ganduje ce a siyasa kuma dole a bi shi.
Tsagin NNPP ya nemi gafarar shugaban kasa Bola Tinubu, Abdullahi Ganduje da dukkan 'yan APC kan kalaman da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kan sauya sheka.
Salihu Tanko Yakasai ya ce Rabi'u Musa Kwankwaso na da zaɓi uku a siyasa: shiga APC ƙarƙashin Ganduje, haɗa kai da Atiku ko ci gaba da zama a NNPP.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ba shi da niyyar tsayawa takarar gwamnan Kano ko Sanata a 2027, yana mai cewa ya fi karkata ga hidimar jama'a.
Jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba shi da alaƙa da sanarwar da ke nuna yana shirin shiga haɗaka.
Bayan NNPP ta rasa manyan jiga-jiganta zuwa APC, shugaban jam'iyyar a kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya ce Rabi’u Kwankwaso ba ɗan jam’iyyar ba ne tun 2023.
A wannan labarin, KNIYA ta bukaci Sanata Barau Jibrin ya tsaya takarar gwamna a 2027, tana mai cewa yana da nagarta da hangen nesa don dawo da martabar Kano.
Siyasar Kano
Samu kari