Garzali Obasanjo Ya Koma NNPP bayan Mafarki da Kwankwaso a Aljanna

Garzali Obasanjo Ya Koma NNPP bayan Mafarki da Kwankwaso a Aljanna

  • Garzali Musa da aka fi sani da Obasanjo ya koma jam’iyyar NNPP bangaren Rabiu Kwankwaso bayan ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya a baya
  • Ya ce addu'o’in da ya yi a kwanakin Zul Hijja ne suka sa ya gane gaskiya, inda ya bayyana cewa mafarki ya nuna masa yana tare da Kwankwaso a aljanna
  • Masu ruwa da tsaki a Kwankwasiyya sun nuna farin ciki da dawowarsa, suna fatan hakan zai kawo ci gaba da haɗin kai a jam’iyyar NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Hon. Garzali Musa Muhammad wanda aka fi sani da Garzali Obasanjo, ya koma jam’iyyar NNPP tare da dawowa tafiyar Kwankwasiyya da ya fice daga cikinta a baya.

Wannan matakin nasa ya haifar da martani masu yawa daga cikin magoya bayan jam’iyyar NNPP da kuma Kwankwasiyya a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Obasanjo
Obasanjon Kwankwasiyya ya dawa NNPP. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garzali Obasanjo ya yi mafarki da Kwankwaso

Garzali ya bayyana cewa ficewarsa daga tafiyar a baya ya samo asali ne daga abin da ya kira “asiri”, wanda ya ce ya shafe shi na wani lokaci har ya manta da daɗin tafiyar Kwankwasiyya.

Shafin Arewa Update ya wallafa bidiyon Obasanjo a Facebook, inda ya ce addu’o’in da ya dage da yi a kwanaki 10 na Zul Hijja ne suka buɗe masa ido ya gane kuskuren.

A cewarsa, ya yi mafarki yana tare da Rabiu Musa Kwankwaso a aljanna, lamarin da ya sa ya ɗauki matakin komawa cikin tafiyar tare da bayyana goyon bayansa ga Abba Kabir Yusuf.

Kwankwasiyya ta karɓi Garzali Obasanjo a NNPP

Hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Salisu Yahaya Hotoro, ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar Garzali cikin tafiyar Kwankwasiyya.

A sakon da ya wallafa a Facebook, Salisu Yahaya ya ce bai dace mutum irin Garzali da suka sha wahala da shi ba ya raba hanya da Kwankwaso.

Haka nan wani mamba a tafiyar, Makama Fagge, ya rubuta a kafar sada zumunta cewa dawowar Garzali ta dace kuma suna fatan hakan zai zama alkhairi ga tafiyar baki ɗaya.

Abdulhadi Yahya kuwa ya bayyana cewa wasu mutane suna barin hanya mai kyau saboda son zuciya, yana fatan Allah ya tsare su daga irin hakan.

Abba Kabir
Obasanjon Kwankwasiyya ya yaba wa Abba Kabir. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Korafi kan dawowar Obasanjo NNPP

Sai dai ba kowa ne ya nuna farin ciki da dawowar Garzali Musa ba, wasu daga cikin magoya bayan Kwankwasiyya sun nuna damuwa da irin kalaman da ya rika furtawa a baya.

Auwal Adam Jogana ya bayyana cewa asiri aka masa kuma yanzu ya warke, yana masa barka da dawowa.

Amma Yakubu Inuwa Kari ya ce bai ji daɗin dawowarsa ba saboda irin cin mutuncin da ya rika yi wa Kwankwaso da Gwamna Abba a baya.

Minista a gwamnatin Buhari ya fita daga APC

A wani rahoton, kun ji cewa minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya sheka.

Mohammed Hassan Abdullahi ya bayyana cewa ya sauya sheka daga APC ne a cikin wata wasika da ya fitar.

Ana rade radin cewa tsohon ministan muhallin zai bayyana jam'iyyar da zai koma domin shiga takarar jihar Nasarawa a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng