Shugaban Sojojin Najeriya
A yau Talata ne mu ka samu rahoto cewa Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan diyyar masu taron Mauludin da harin bom daga jirgin soja ya kashe a Jihar Kaduna.
Kungiyar dattawan arewa ta bukaci gwamnati da ta gudanar da cikakken bincike kan harin da sojoji suka kai wa masu maulidi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri.
Wani mutumin Kaduna ya ce a danginsa kaɗai sun rasa wajen mutum 34 da aka sa bam. Shaidu sun bayyana abin da suka gani bayan wani jirgin sama ya jefa bam a maulidi
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai wa musulmi a yayin bikin Mauludi.
Rahoton shelkwarar soji ya nuna cewa dakarun soji sun kashe sama da 'yan ta'adda 180, sun cafke 204 yayin da suka kubutar da mutum 234 da aka yi garkuwa da su.
Mazauna wani gari da ke karkashin Birnin Gwari, jihar Kaduna, sun tsere daga gidajensu don tsira da rayukansu bayan da aka janye sojojin da aka girke a garin.
Babban kwamanda janar na rundunar soji, Yerima Kure ya riga mu gidan gaskiya bayan shekaru 84 a duniya. Shi ya jagoranci dakarun da suka murkushe Maitatsine a Kano.
Aikin ceto da dakarun sojoji karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut suka yi a jihar Sokoto ya yi sanadiyar ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su.
An yi ba ta kashi a sanyin safiyar ranar Laraba tsakanin rundunar 'yan sanda da sojoji a Yola, babban birnin jihar Adamawa,an kashe sufetan 'yan sanda.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari