Ku Zo Ku Siya: An Saka Jirgin Shugaban Najeriya a Kasuwa, Ana Neman Mai Saye

Ku Zo Ku Siya: An Saka Jirgin Shugaban Najeriya a Kasuwa, Ana Neman Mai Saye

  • Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta sanya jirginta na Falcon 900B a kasuwa kan dalar Amurka, inda take neman mutane su taya
  • NAF ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ce ta amince da sayar da jirgin kirar Falcon 900B
  • Yan Najeriya sun yi tsokaci kan shirin rundunar sojin na sayar da Falcon 900B a kan kudin dalar Amurka mai makon kudin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta yi kira ga masu sha'awar sayen jirginta na Falcon 900B da su wasa wukarsa, domin ta sanya shi a kasuwa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter) @NigAirForce.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta kare matakin kai harin bam kan masu Maulidi, ta fadi dalilanta

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da sayar da jirgin Falcon 900B
A cewar rundunar sojin saman Najeriya, gwamnatin tarayya ce ta amince a cefanar da jirgin shugaban kasar na Falcon 900B. Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, gwamnatin tarayya ce ta amince a cefanar da jirgin shugaban kasar na Falcon 900B, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me masu sha'awar sayen jirgin za su yi?

Masu sha'awar sayen jirgin za su gabatar da bukatar hakan kai tsaye a sashen saye da sayar da kayayyaki na shelkwatar rundunar ko kuma ta hanyar adireshinta na yanar gizo.

Rundunar ta ce za a rufe karfar tayin sayen jirgin a ranar 24 ga watan Disamba, 2023, don haka masu sha'awa sai su hanzarta, Legit ta ruwaito.

Haka zalika, ana sanar da masu sha'awar sayen jirgin da su fadi kudin da za su saya a kudin dalar Amurka (US$) tare da makala sunan hafsan rundunar sojin sama, mai adire shi lamba 7 Garki Area, Abuja, a jikin takardar.

Yan Najeriya sun yi tsokaci kan sayar da jirgin

Kara karanta wannan

Rundunar sojin sama ta yi martani kan zargin kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna, ta roki jama'a

@ezechukwumicha4

Gwamnatin tarayyar Nigeriya na sayar da jiragen sama, gaskiya na damu matuka.

@dj_gabson

A sayar da shi kawai don sayo jiragen yaki na zamani kamar f-35 da dai sauransu.

@MartGodswill

Ina fatan dai mutum na iya biya da kadan-kadan?
Domin na sami Tufaif guda ɗaya da nake ajiyewa tun watan Janairu don siyan Polo don Kirsimeti!
Idan kun amince sai na tura maku shi kawai, irin wannan harkar ba a jira.

@lekeyor

Nawa muke da su da muke sayarwa yanzu?
Nawa ne daga cikin mutanenmu za su iya sarrafa wannan jirgin?

@knotcase

Gwamnatin Najeriya na sayar da kadarori ga jama'a a cikin dalar Amurka? Ta yaya muka shiga cikin wannan hali?

@nichybest_trade

Sanya jirgin sama don siyarwa alama ce da ke nuna cewa akwai matsala a tattalin arzikin Najeriya.

Ɗangote zai siyar da katafaren jirgin alfarmarsa

A wani lamarin mai kama da wannan, attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya shirya sayar da katafaren jirgin sama mai zaman kansa da ya biya miliyoyin daloli domin mallakarsa.

Dangote ya sayi katafaren jirgin domin amfanin kansa shekaru 13 da suka gabata domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, amma yanzu yana son sayar da shi, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel