Gwamnatin Tinubu Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

Gwamnatin Tinubu Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

  • Muhammad Badaru Abubakar ya ce gwamnatin tarayya za ta biya diyya ga dangogin wadanda bam ya kashe a Kaduna
  • Kwanan nan sojojin sama su ka yi kuskuren kashe wasu masu maulidi a kauyen Tudun Birni da ke karamar hukumar Igabi
  • Ministan tsaro ya dauki alkawari za a gudanar da bincike na musamman kumaa biya diyyar jinin da aka rasa ta kuskure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta biya diyya ga dangin mutanen da sojoji su ka hallaka ta hanyar kuskure a jihar Kaduna.

Muhammad Badaru Abubakar wanda shi ne babban Ministan tsaro na kasa, ya bada wannan tabbaci kamar yadda Aminiya ta rahoto dazu.

Kara karanta wannan

Maulidi: Atiku ya yi martani kan harin bam da aka yi kan bayin Allah a Kaduna, ya ba da shawara

Bola Tinubu
Za a binciki kisan sojoji a Kaduna Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ministan tsaro ya ce akwai diyya

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya yi magana ne bayan Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi umarni a binciki abin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce ma’aikatarsa za ta hada-kai da gwamnatin jihar Kaduna domin yin cikakken binciken yadda jirgin sojoji ya kashe Bayin Allah.

Hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa, ta tabbatar da mutum 85 aka rasa a sanadiyyar kuskuren da sojoji su ka yi wajen sakin bam.

Kaduna: Kungiyar Dattawan Arewa

Kafin Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka, kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta bukaci a biya diyya na duk rayukan da aka rasa.

21st Century Chronicle ta rahoto Farfesa Tukur Muhammad-Baba wanda shi ne Kakakin ACF ya ce kyau a biya jinin wadanda da aka kashe.

Danyen aikin sojoji a Kaduna ya fusata al'umma

Kara karanta wannan

Kisan masu maulidi a Kaduna: Dattawan Arewa sun magantu, sun ba gwamnati sharudda

Ganin irin wannan kuskure ya faru da mutane a Borno, Yobe, Nasarawa, Benuwai da Zamfara, hakan ya fusata wasu manya da malaman Arewa.

Kafin Ministan ya sanar da hakan, shugaban hafsun sojoji ya ziyarci garin Kaduna.

A dakata da taron Izala - MSS

Legit ta samu labari kungiyar Musulman dalibai watau MSS ta reshen Zariya ta bukaci kungiyar Izala ta dakatar da shirya wa’azinta na kasa.

Ganin abin da ya faru ga masu maulidi, shugaban kungiyar, Hussain Muhammad Gamawa ya ce a tsaida taron JIBWIS zuwa wani lokaci tukun.

Sojoji sun kashe mutane 34 a dangi guda

Kamar yadda labari ya zo, akwai mutumin da ya rasa ‘yanuwa 34 sannan akwai mutane 66 da ke gadon asibitin Barau Dikko a cikin danginsu.

Mutanen Tudun Biri da aka zanta da su, sun ce sau biyu aka jefo masu bam ta jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel