A Dangi 1 Kadai, Sojoji Sun Kashe Mutane 34 da Bama Bamai a Wajen Maulidin Kaduna

A Dangi 1 Kadai, Sojoji Sun Kashe Mutane 34 da Bama Bamai a Wajen Maulidin Kaduna

  • Idris Dahiru ya na cikin wadanda su ka rasa ‘yanuwa a abin da ya faru da masu maulidi a Tudun Biri a Kaduna
  • Wannan mutumi ya shaidawa duniya yadda a lokaci guda su ka rasa sama da mutane 30 daga cikin danginsu
  • Wata mata ta ce a lokacin da aka yi masu luguden wutan, gwamnati da sojoji ba su iya turo masu jami’ansu ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Idris Dahiru wani mazaunin Tudun Biri ne a karamar hukumar Igabi, inda sojoji su ka hallaka Bayin Allah.

A sakamakon jefa bama-bamai da sojojin kasa su ka yi a garin Kaduna, mutane fiye da 100 ake tunanin sun mutu.

Jirgin sojoji
Wani Jirgin sojoji ya kashe mutane a Kaduna Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An rasa rayuka 34 a dangi guda a Kaduna

Kara karanta wannan

"Ban ji dadi ba": Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi a Kaduna, ya bayar da wani umurni

BBC Hausa ta zanta da Malam Idris Dahiru wanda ya shaida mata yadda sojoji su ka harbo masu bam daga jirgin yaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Malam Idris Dahiru, ana taron maulidi da aka shirya domin Annabi Muhammad SAW aka jefo masu bam.

Ba a gama dauke wadanda bam din ya yi sanadiyyar jikkatawa ba, sai aka sake harbo wani sabon bam din bayan minti 30.

Kamar yadda ya shaidawa gidan rediyon, Dahiru ya ce masu taron addin sun ji saukar bam ne ba tare da ankara ba.

Sojoji sun harbowa mutane bama-bamai 2

Abin da sojoji su ka kira kuskure ya shafi kananan yara da mata a kauyen Tudun Biri.

Mutanen da su ka garzayo domin ceton wadanda masifar ta fara auka masu, su ne su ka mutu da aka harbo na biyun.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya tsokano Rigima da ikirarin babu aikin da Buhari ya yi a shekara 8

Wannan Bawan Allah ya ce a danginsa kurum, mutane 34 su ka rasu, baya ga ‘yanuwa 66 da su ke gadon kwance.

A cewarsa an kwatar da wadanda su ka samu rauni a asibitin Barau Dikko a Kaduna yayin da aka umarci ayi bincike.

Yadda sojoji su ka kashe mutane - 'Yar Tudun Biri

Wata Baiwar Allah ta bada labarin yadda abin ya faru, ta ce da almuru kurum su ka ji shawagin jirgin saman sojoji.

Aisha ta ce bayan sojojin sun saki bam ga wadanda ke taron maulidin, bayan mintuna 30 aka sake harbo wani.

A cewar matar, babu wadanda su ka kawowa mutanenta ceto illa jami’an KADGIS.

Mutane sun yi tir da sojoji kan harin Kaduna

Ana da labari Isa Ali Ibrahim Pantami ya bukaci ayi bincike a hukunta sojojin da su ka kashe masu addini a Kaduna.

Irinsu Bashir Ahmaad sun yi kaca-kaca da sojoji a dalilin kuskuren dasa bam ga masu bikin maulidin a Igabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel