An Yi Musayar Wuta Tsakanin ’Yan Sanda Da Sojoji, an Kashe Wani Sufeta a Adamawa

An Yi Musayar Wuta Tsakanin ’Yan Sanda Da Sojoji, an Kashe Wani Sufeta a Adamawa

  • An yi ba ta kashi a sanyin safiyar ranar Laraba tsakanin rundunar 'yan sanda da sojoji a Yola, babban birnin jihar Adamawa
  • A yayin ba ta kashin ne sojoji suka harbi wani sufetan 'yan sanda, lamarin da ya zama ajalinsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana
  • Sai dai, rundunar soji ta ce sojoji sun je shelkwatar 'yan sandan ne don karbo jami'in su da suka yi zargin 'yan sanda sun harba kuma sun boye shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yola, jihar Adamawa - Shelkwatar 'yan sanda a jihar Yola a sanyin safiyar yau ya zama tamkar filin yaki, inda sojoji makare a motoci 12 suka bude wuta, har suka kashe sufetan 'yan sanda, Jacob Daniel.

Kara karanta wannan

Yadda muka sha kaye a zaben 1998 domin na ki bai wa INEC cin hanci, Obasanjo

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Afolabi Babatola ya yi Allah wadai da irin wannan farmakin da sojojin suka kai wa 'yan sanda, ya kuma gargade su kan kiyaye faruwar hakan nan gaba.

Sojoji da 'yan sanda sun yi arangama a Yola
An yi ba ta kashi a sanyin safiyar ranar Laraba tsakanin rundunar 'yan sanda da sojoji a Yola, lamarin da ya yi ajalin sufetan 'yan sanda. Hoto: @HQNigerianArmy/@PoliceNG
Asali: Twitter

Sojoji da 'yan sandan, sun yi arangamar ne a sha tale-talen Target, karamar hukumar Yola ta Arewa, lamarin da ya jawo asarar ran sufetan 'yan sanda Daniel.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba za mu lamunci kashe mana jami'i ba - Kwamishinan 'yan sanda

The Tribune ta ruwaito cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, ya bayar da umurnin gudanar da bincike, don wanzar da zaman lafiya da yin adalci.

Kwamishina Babatola ya yi gargadin cewa kai wa kowanne jami'i farmaki yayin da yake a bakin aiki babban laifi ne, kuma hukumar ba za ta lamunci hakan ba.

Da ya ke ba da tabbacin yadda hukumar ta ke martaba rayuwar jami'anta, kwamishinan ya ce dole za su bi matakan doka don bin kadin jami'in da aka kashe, The Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An sake kama hatsabibin dilallin kwayoyi shekaru 7 bayan tserewarsa daga gidan yari a Abuja

Dalilin zuwan sojoji shelkwatar 'yan sandan Adamawa

Da 'yan jarida suka tuntubi kwamandan bataliyar soji ta 23, Birgediya Janar Gambo Mohammed kan lamarin, ya ce su jami'an 'yan sanda ne suka harbi wani soja tare da boye shi, wannan ya sa sojojin suka je karbo shi.

Sai dai wani jami'in dan sanda ya shaidawa Tribune cewa an garzaya da wani jami'in soji sanye da kayan gida zuwa asibitin Modibbo Adama da ke Yola.

Ya ce ba su boye jami'in da aka ji wa rauni ba, sabanin ikirarin da hukumar 'yan sandan ta ke yi.

Mutane 37 Sun Mutu Wurin Neman Shiga Aikin Soja a Kasar Congo

A kasar Congo kuwa, kun ji yadda akalla matasa 37 ne suka mutu sakamakon wani turmutsutsu da ya barke a filin wasa na Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo.

Matasan sun je filin ne domin a tantance su a wani shiri da hukumar sojin kasar ke yi na daukar matasa 1,500 aiki, lamarin da ya jikkata mutane da dama, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel