Labaran tattalin arzikin Najeriya
Hukumar ICPC ta kame wani manajan banki d ake boye sabbin Naira a cikin na'urar ATM don kawai mutane kada su samu sabbin Nairan da ake faman layi a kansu yanzu.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da sauya fasalin takardun naira saboda rashin cimma muradinsa na takarar Shugaban Kasa.
An samu labarin yadda jami'an hukumar EFCC suka kama wata mata bisa zargin ta dauko sabbin kudade ta yi likinsu a gidan biki yayin da ake ci gaba da jira kudin.
Shehu Sani ya yi kaca-kaca da gwamnan CBN da kuma manufarsa ta ganin daina amfani da kudade a hannun jama'a a wannan zamanin. Shehu Sani ya ce hakan bai yi ba.
Wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta inda aka ga wani mutum yana dauke da POS yana yawo dashi lokacin da yake tallan rake. Mutane sun siya sun biya shi.
Gwamnonin jam'iyyar APC mai ci sun ce babu ruwansu da halin da ake ciki, za su dauki mataki kan batun da ya shafi sabbin Naira, kuma zasu gana da Buhari a yau.
A labarin da muke samu, wani mutum ya bayyana ya rasa matarsa yayin da ya je neman sabbin kudi don mata jinya amma ya gaza samun yadda zai cire a bankuna kasa.
A halin da ake ciki, 'yan Najeriya sun mamaye bankunan kasar nan saboda nuna bacin ransu da yadda ake hana su sabbin Naira. An ga wanda ya kutsa kai cikin CBN.
Labarin da muke samu ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa Kwankwaso ya ce babu wanda zai iya hana dan takarar shugaban kasa a Najeriya sabbin Nairan nan.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari