Canza Naira: Shugaban Majalisa Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Kafin Zabe

Canza Naira: Shugaban Majalisa Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Kafin Zabe

  • Shugaban majalisar wakilai yana cikin wadanda suka soki tsarin sauyin kudi da bankin CBN ya kawo
  • Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa muddin ba ta canza zani ba za su dauki mataki a kai
  • Gbajabiamila ya fadawa mutanen mazabarsa cewa Majalisar tarayya za ta iya yin gaggawa kan lamarin

Abuja - Shugaban majalisar wakilan tarayya ya bayyana cewa idan bankin CBN bai kawo karshen wahalar da mutane ke sha ba, za su koma bakin aiki.

A halin yanzu ‘yan majalisa sun tafi hutu, amma This Day ta rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana barazanar cewa za a bude majalisar wakilan kasar.

Shugaban majalisar tarayyan yake cewa za su cigaba da sa wa Godwin Emefiele ido a kan batun canjin manyan takardun Naira da babban bankin CBN ya yi.

Kara karanta wannan

Sauya Kudi: Da Gaske Gwamnan CBN Na Son Haddasa Rudani a Zaben 2023? Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu

Femi Gbajabiamila ya yi zama ne da kabilu dabam-dabam da ke zaune a mazabar da yake wakilta watau Surulere a jihar Legas a cikin karshen makon nan.

Meya hana a cafke Emefiele?

A wajen wannan tattaunawa, ‘dan majalisar ya ce abin ya kai saura kiris ya sa hannu a takardar bada izinin cafke Emefiele saboda kin hallara a gabansu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta rahoto shugaban majalisar yana cewa sun yi ta aikawa Gwamnan babban bankin takarda domin su gana da shi, amma ya ki zuwa gaban kwamiti.

Shugaban Majalisa
Shugaban Majalisa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Facebook

“Majalisar wakilan tarayya tayi ta tsoma baki a lokuta dabam-dabam. Mun gayyaci Gwamnan CBN ba sau daya ba, amma ya gagara zuwa ya amsa.
Saboda yana tsoron mu na da tambayoyi masu zafi da za mu yi masa. Har sai da ta kai zan sa hannu a takardar bada izinin cafke shi (Emefiele).

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Karya Kawai Ya Shararawa Shugaba Buhari: Babban Hadimin Shugaban Kasa

Da an kafa tarihi, ya zama karon farko da za a cafke Gwamnan CBN. Saura kiris in yi hakan."

- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila

A rahoton Leadership, Gbajabiamila ya ce saboda CBN na cin gashin kan shi, wannan ba zai hana majalisar wakilan tarayya ta bada umarnin cafke wani ba.

A game da batun canjin kudi, ‘dan siyasar ya ce an jefa al’umma a matsin lamba, masu kudi ba su da hanyar cin abinci a dalilin tsarin da aka fito da shi.

‘Dan majalisar yake cewa su na tare da ‘dan takaran APC, Bola Ahmed kan matsayar da ya dauka, kuma za a iya yin zaman gaggawa idan ta kama kafin zabe.

Banki ya boye N6m a Ekiti

Makonni biyu da suka wuce CBN ya ba wani banki sababbin takardun kudin da aka buga. Rahoto ya zo har yau ma’aikatan bankin nan ba su fito da kudin ba.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

Ana zargin ma’aikatan bankin da ke garin Ado Ekiti sun boye miliyoyi a lokacin da ake wahala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel