Ka Magance Karancin Sabbin Naira a Yanzu, Sanata Ya Roki Shugaba Buhari

Ka Magance Karancin Sabbin Naira a Yanzu, Sanata Ya Roki Shugaba Buhari

  • Wani sanata ya bayyana bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta kawo karshen karancin sabbin Naira
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi yayin da aka sauya kudade tare da kirkirar wasu
  • CBN ya ce akwai kudi, amma bankuna sun ki zuwa su dauka, lamarin da ya rikita kowa a kasar nan

Abuja - Shugaban kwamitin babban birnin tarayya a majalisar dattawa, Sanata Smart Adeyemi ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya duba tare da kawo mafita ga matsalar karancin sabbin Naira a kasar yanzu.

Sanatan ya ce, ya kamata shugaban kasan ya duba ya kuma rage wa'adin da yace zai tabbatar da kawo karshen karancin sabbin kudi cikin kwanaki bakwai domin kaucewa mutuwar ‘yan kasa.

Sanata ya nemi Buhari ya farka
Ka Magance Karancin Sabbin Naira a Yanzu, Sanata Ya Roki Shugaba Buhari | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sanatan, wanda ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Toh fa: CBN na kuntatawa talakawa da sunan hukunta 'yan rashawa, inji sanata Shehu Sani

Kwana bakwai sun yi yawa

Buhari a ranar Juma’a ya yi alkawarin kawo mafita ga matsalar karancin Naira da ‘yan kasar ke fuskanta cikin kwanaki bakwai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari ya yi wannan alkawarin ne lokacin da ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Amma Adeyemi ya ce, halin da ‘yan kasar nan ke ciki ba abu ne da ya kamata ya ci gaba da faruwa, inda ya roki Buhari da ya taimaka ya kare ‘yan kasar daga halaka.

Ya kuma bayyana cewa, Buhari bai san halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba bisa wannan karanci na sabbin kudi.

Ya kuma yabawa Buhari da cewa, a matsayinsa na shugaban da ke son 'yan kasa da ci gaban kasar, ya kamata ya gaggauta kawo mafita kafin kwanaki bakwai da ya diba ma kansa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Bayyana 'Yan Najeriya Kwanakin da Za a Kwashe Kafin Matsalar Sabbin Kudi Tazo Karshe

Akwai kudi a bankuna, ba sa son ba 'yan Najeriya

A wani labarin, kunji yadda CBN yace akwai kudade a hannun bankuna, amma ba sa son ba talakawa da ke bukata.

CBN ya bayyana hakan ne lokacin da 'yan kasa ke kukan ba sa samun kudi a ATM da kanta idan suka je banki.

Tun da aka buga sabbin kudade a Najeriya kasar ta zama kullum cikin rikici, an rasa a ina matsalar take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel