Kayan Mata Nake Sha Don Cin Kudin Wasu Sanatocin Najeriya, Inji ’Yar Tambaden BBNaija

Kayan Mata Nake Sha Don Cin Kudin Wasu Sanatocin Najeriya, Inji ’Yar Tambaden BBNaija

  • Wata fitacciyar ‘yar wasan tambade ta bayyana yadda ta cin kudin manyan mutane a Najeriya; ciki har da sanatoci
  • Wannan na zuwa ne lokacin da take magana da wasu abokanta a tattaunawar gefen shirin BBNaija da aka fara kwanan nan
  • Ta ce tana amfani da kayan mata domin daukar hankalin mutanen da ke kiranta da sunan rakiya a kasar nan don biyanta kudi

Najeriya - Wata ‘yar wasan tambade na Big Brother Titans mai suna Nana ta bayyana yadda take samun kudin da suka amsa sunan kudi ta hanyar amfani da kayan mata kafin ta shigo shirin.

Ta bayyana cewa, a baya tana bin maza; musamman manya ciki kuwa har da wasu sanatocin Najeriya a matsayin ‘yar rakiya zuwa shakatawa don samun na kashewa.

Da take magana tare da sauran abokanta na shirin BBNaija; su Yvonne, Jenni O, Maya da Olivia, ta bayyana tasirin kayayyakin tada sha’awa da karin ni’ima na mata da take amfani dasu.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Gwamnonin APC sun tubure, za su gana da Buhari su fada masa abu daya

Amfani kayan mata nake na ci kudin sanatocin Najeriya, inji wata budurwa
Kayan Mata Nake Sha Don Cin Kudin Wasu Sanatocin Najeriya, Inji ’Yar Tambaden BBNaija | Hoto:yabaleftonline.ng
Asali: UGC

Nana ta bayyana rayuwarta ta baya gabanin shiga shirin BBNaija, inda tace ta samu manyan kudaden da ba a tsammani ta sanadiyyar bibiyar maza.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ni ‘yar rakiya ce ga manyan mutane, kuma suna kwanciya da ni su ba ni kudi, inji Nana

A cewarta, ta kasance ‘yar rakiya ga manyan mutane, kuma tana kwanciya dasu; ciki har da sanatocin kasar nan da bata bayyana suna ba.

Ta ce tana amfani kayan mata domin daukar hankalin masu nemanta, kuma hakan ya yi tasiri, domin daga zama ‘yar rakiya ta kwanta da manyan mutane da yawa kuma ta tara manyan kudade.

Daga nan Nana tace, yanzu kam ta sake wayewa, saboda haka manyan mutanen da suke neman kwanciya da ita su shirya, inda ta fito daga wasan tambade na BBNaija za ta zo musu da tsaraba.

Kara karanta wannan

Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi

Ku shirya, zan dawo

Shirin BBNaija wani shiri ne da ake yi, wanda ke ba ‘yan wasan damar duk abin da suka ga dama, ciki har da kwanciya da juna.

Sanannen abu ne yadda mata a Najeriya ke yawan amfani da kayan mata, kuma matan manyan mutane da fitattun mutane su ne kan gaba.

A shekarar da ta gaba ne aka yi dambarwa tsakanin Jaruma mai kayan mata da Regina Daniel kan kitimurmurar da ta shafi maganin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel