Gwamna Ya Sayi Hannun Jari a Kamfanin Dangote, Za a Raba Wa Mutane Kyauta

Gwamna Ya Sayi Hannun Jari a Kamfanin Dangote, Za a Raba Wa Mutane Kyauta

  • Gwamnatin Zamfara ta amince da shirin bai wa mazauna jihar 36,176 hannun jari a rukunin kamfanonin Dangote domin bunƙasa tattalin arziƙi
  • Kowane wanda zai amfana ana sa ran zai samu kusan hannun jari 20 ta hanyar shirin sayar da hannun jarin matatar Dangote ga jama’a
  • Za a zaɓi waɗanda za su amfana daga ƙananan hukumomi 14 na jihar, inda Gusau za ta samu kaso mafi yawa na mutane 4,522

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta amince da wani shiri na bai wa mazauna jihar 36,176 hannun jari a rukunin kamfanonin Dangote.

Gwamnatin karkashin Gwamna Dauda Lawal ta yi haka ne a wani mataki na bunƙasa shigar jama’a harkokin kuɗi da kuma ƙarfafa tattalin arzikinsu.

Dauda Lawal
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal yana jawabi a taron Majalisar zartarwa Hoto: Dauda Lawal
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Agajin Gaggawa ta jihar Zamfara ta tabbatar da hakan a Gusau.

Kara karanta wannan

Gwamna ya saya wa dubban matalautan mata hannun jarin matatar Dangote

Yadda gwamnatin Zamfara ta tsara shirin

Ma'aikatar ta ce an tsara shirin ne domin bai wa Zamfarawa damar shiga harkokin zuba jari da cin moriyar damammakin da ake da su a ɓangaren kasuwanci a ƙasar.

A ƙarƙashin shirin, ana sa ran kowane wanda zai amfana zai samu kusan hannun jari 20 a shirin matatar Dangote na sayar da hannayen jari ga jama’a, wato Initial Public Offering (IPO).

Za a gudanar da shirin tare da haɗin gwiwar ma’aikatun Harkokin Jinƙai da Agajin Gaggawa da Kuɗi na jihar, da kuma Kamfanin Zuba Jari na Zamfara.

Kwamishinan Harkokin Jinƙai, Salisu Musa Tsafe Kainuwa, ne zai jagoranci gudanar da shirin.

Yadda za a raba hannun jarin

Ma’aikatar ta bayyana cewa za a zaɓi waɗanda za su amfana daga ƙananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

Za a ware mutum 2,261 ga kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 13, yayin da Gusau, babban birnin jihar, za ta samu mutum 4,522.

Kara karanta wannan

Jerin jihohi 12 da Shugaba Tinubu zai iya zuwa kamfe kafin babban zaben 2027

Ta kuma ce shirin zai haɗa da masu buƙata ta musamman, a wani mataki na tabbatar da cewa kowa ya samu damar cin moriyarsa.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ma’aikatar ta ƙara da cewa Gwamna Dauda Lawal ne ya amince da shirin domin faɗaɗa damar mazauna Zamfara ta fuskar zuba jari da kuma inganta dogaro da kai ta fuskar kuɗi.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce shirin na daga cikin manyan tsare-tsarenta na jinƙai da bunƙasa tattalin arziƙi. Ta kuma bayyana cewa ana sa ran sanar da wasu shirye-shirye da za su shafi mata da matasa.

Za a rabawa mata hannun jari a Gombe

Kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ware miliyoyin Naira domin sayen hannayen jari a matatar Dangote ga mata.

Gwamnan ya amince da sayen hannayen jari a matatar Dangote ga mata 28,284 masu rauni a faɗin jihar Gombe.

Gwamnatin Gombe da gidauniyar Aliko Dangote za su bai wa kowace mace hannayen jari 20 domin inganta tattalin arzikinta da rage talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262