Shirin Gwamnatin Tinubu Bayan Wa’adin Rangwame Farashin Fetur Ya Ƙare

Shirin Gwamnatin Tinubu Bayan Wa’adin Rangwame Farashin Fetur Ya Ƙare

  • Gwamnatin tarayya za ta tantance rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur da NNPCL ta fara, domin sanin ko akwai buƙatar ƙarin tallafi
  • Ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin fetur ya taimaka wajen kauce wa ƙarancin mai, tare da samar da damar zuba jari
  • Oyedele ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin inganta rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar samar da ayyukan yi, tallafin karatu da lamunin ƙananan kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta shirya nazarin shirin rangwamen kuɗin fetur da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya ƙaddamar, bayan kwanaki 30 domin sanin matakin gaba.

Rahotanni sun bazu ranar Juma’a cewa Taiwo Oyedele, ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, ya ce gwamnati za ta yanke shawarar ko akwai buƙatar ƙarin mataki bayan nazarin sakamakon shirin.

Kara karanta wannan

An hura wa Tinubu wuta kan 2027, ana so ya hakura da shiga takara

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan saukaka farashin fetur
Shugaba Bola Tinubu yayin taron majalisar zartaswa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu za ta duba rangwamenl

Da yake tabbatar da bayanin Oyedele, Efe Ovuakporie, daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar kuɗi, ya shaida wa TheCable cewa ana sa ran NNPCL zai tantance shirin, sannan ya miƙa rahotonsa ga gwamnati.

Ovuakporie ya ce rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur ya fara ne a matsayin shirin tallata kayayyaki na NNPCL domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Sai dai daga baya gwamnati ta yanke shawarar amfani da shirin wajen rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa na ɗan lokaci, musamman masu harkar sufuri.

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan farashin fetur
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Oyedele ya bayyana amfanin cire tallafin fetur

Haka kuma, Oyedele ya ce cire tallafin fetur ya taimaka wa Najeriya wajen kauce wa matsalolin samun mai a lokacin rikicin duniya, tare da samar da yanayin da ya ba da damar zuba jari kamar matatar Dangote.

Ya ce:

“Da ba mu cire tallafin fetur ba a yau, da rikicin da ake fama da shi a duniya ya sa muna fama da matsalar samun mai. Da matatar Dangote ba za ta wanzu ba, domin gyare-gyaren da muka yi ne suka samar da yanayin da ya ba da damar zuba jarin."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba

Ministan ya ce babban abin da gwamnati ta sa gaba a yanzu shi ne hanzarta ganin amfanin gyare-gyaren tattalin arzikin ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa ’yan Najeriya, da kuma inganta yanayin kasuwanci ga ’yan kasuwa.

Oyedele ya bayyana cewa samar da wutar lantarki da inganta sufuri za su taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa kasuwanci, tare da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya isa wuraren da suke son zuwa.

Ya ce an tsara gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnati ne domin amfanar talakawan Najeriya, duk da matsalolin da wasu daga cikin manufofin suka jawo wa jama’a.

Hadimin Davido zai goyi bayan Atiku

Kun ji cewa hadimin mawaki Davido da ake kira Israel DMW ya yi magana game da zaben 2027 tsakanin Bola Tinubu da yan adawa.

Israel wanda manajan harkokin sufuri na mawaki Davido ne ya nuna goyon bayansa ga Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya bayyana cewa mulkin ɗan Arewa ya fi dacewa, tare da sukar kwangilar Naira tiriliyan 15 da aka bai wa mutum guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.