Bidiyon Mai Rake da Karbar Kudinsa Ta POS Ya Ba da Mamaki, Jama’a Sun Bayyana Fushi

Bidiyon Mai Rake da Karbar Kudinsa Ta POS Ya Ba da Mamaki, Jama’a Sun Bayyana Fushi

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yada bidiyon wani mai tallan rake da ya bi sabuwar dokar takaita rike kudi da gwamnati ta kawo
  • An ga mutumin dauke da injin POS a lokacin da yake talla a baro ga kwastomomi sun zagaye shi suna saye
  • ‘Yan Najeriya a kafar Twitter sun shiga mamaki, wasu kuma sun nuna fushi ya yadda bankin ke wahala ‘yan Najeriya babu gaira babu dalili

Najeriya - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nunawa ‘yan Najeriya yadda mai tallan rake ya bi ka’ida da sabuwar dokar takaita rike kudi ta Najeriya.

A wani bidiyon da bankin ya yada a Twitter, an ga wani mutumin da ke tallan rake yana rike da na’urar POS yana tura baron tallan rakensa.

Kwastomin da ke siyan raken sun zagaye suna yi masa tambayoyi, wani kuma ya siya rake yana saka lambobin ‘PIN’ dinsa don biyan kudi a POS.

Kara karanta wannan

Toh fa: CBN na kuntatawa talakawa da sunan hukunta 'yan rashawa, inji sanata Shehu Sani

An rage amfani da kudi, mai rake ya koma karbar kudi da POS
Bidiyon Mai Rake da Karbar Kudinsa Ta POS Ya Ba da Mamaki, Jama’a Sun Bayyana Fushi | Hoto: @zahradeenmseega.
Asali: TikTok

Mutane da yawa ne suka yi layi domin siyan raken nasa, inda shi kuwa cikin kwarin gwiwa yake kasuwancinsa ba tare da nuna damuwa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bamu gamsu ba, inji 'yan Najeriya

Yan Najeriya da yawa sun yi Allah-wadai da yadda CBN ke ba ‘yan Najeriya wahala ta hanyar hana su rike kudade da yawa a cikin al’umma fiye da kima.

Wasu mutane da yawa kuwa sun yi martani tare da yada wasu bidiyoyin da aka fitar na yadda mutane su kokuwa da shan wahalar layi a bankunan kasuwanci a kasar.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’ar Twitter

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin wannan bidiyon na yawo a kafar sada zumunta ta Twitter.

@IamtheOGee:

“Wahalar ta yi yawa, abin ba kyan gani kowa a takure yake da ganin wannan.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Wani Tsohon Attajiri da ya Haukace, Yana Tikar Rawa a Kasuwa Babu Sauti, ya Narka Zukata

@EhiEhidan:

"Ta yaya za a koma biyan kudi da kati bayan komai kayi sai an caje ka? Kowace kasa da ke son rage amfani da tsabar kudi na kira ko kuma neman bankuna su daina caji kan kashe kudi amma banda Najeriya.”

@BalogunREADONE:

"Hakan abu ne mai kyau amma ya kamata bankuna su gyara sabis saboda ba sa iya daukar biyan kudi da yawa..kwanan nan an sha wahala.. da yawan sabis din bankuna daukewa yake.”

@AmaraBlessing_:

"Ya zanyi idan ina son siyan ruwan leda na Naira 10, sai na yi amfani da POS?”

A ra'ayin gwamna El-Rufai, ba ma yanzu ne ya kamata a kawo batun sauya sabbin Naira ba, ko kuma a daga lokacin zuwa gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel