Kotu Ta Hana CBN Tsawaita Wa’adin Amfani da Tsofaffin Takardun Naira

Kotu Ta Hana CBN Tsawaita Wa’adin Amfani da Tsofaffin Takardun Naira

  • An shigar da Buhari, CBN da bankuna a kasar nan kara a gaban kotu kan batun da ya shafi sauya kudi
  • An ce kada CBN ya tsawaita wa'adin amfani da sabbin tsoffin kudi don gujewa abin da ka iya biyo baya
  • A ranar 1o ga watan Fabrairu ne za a daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 bayan kirkirar sabbin kudi

FCT, Abuja - Kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da kada ya kunce damararsa game da wa’adin daina amfani da tsoffin Naira.

Wannan na zuwa ne a cikin wani hukuncin da aka yanke a ranar Litinin 6 Faburairu, 2023 kan kara mai lamba FCT/HC/CV/2234/2023 da aka shigar a gaban kotun, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Gwamnonin APC sun tubure, za su gana da Buhari su fada masa abu daya

CBN, Buhari da sauran bankunan kasar nan ne aka sanya a matsayin wadanda ake kara a cikin takardar da aka kai gaban alkali.

An hana CBN tsawiata wa'adin daina kashe tsoffin Naira
Kotu Ta Hana CBN Tsawaita Wa’adin Amfani da Tsofaffin Takardun Naira | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Abin da hukuncin ke nufi

Mai shari’a Eleojo Enenche na kotun FCT ya umarci CBN da kada ya tsawaita wa'adin 10 ga watan Fabrairu nan da zuwa lokacin da kotu za ta sake duba karar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A hukuncin, alkali ya ce kada CBN ya kuskura ko shi ko ma’aikatansa su dago batun tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000.

Hakazalika, kotun ya ce, ya zuwa lokacin da za a saurari karar, 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin karshe na daina amfani da tsoffin kudaden.

Wannan umarni na kotu zai yi amfani ne na tsawon kwanaki bakwai har zuwa lokacin da za a saurari batun a ranar 14 ga watan Fabrairu, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kada ku sake kara wa'adin daina amfani da Naira, Atiku ga CBN

Wadanda suka shigar da karar sune jam’iyyun Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP), Allied Peoples Movement (APM), da kuma kungiyar siyasa ta National Rescue Movement (NRM).

Kwanaki 7 sun yi yawa, ka yi yanzu, sanata game da sabbin Naira ga Buhari

A wani labarin, wani sanata a Najeriya ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kawo karshen matsalar sabbin Naira.

Sanata Smart Adeyemi ya ce, 'yan Najeriya na dandana azaba wajen samo sabbin Naira, kuma babu kudin banki.

Ya kuma shaida cewa, kwanaki bakwai da Buhari yace ya dauka don magance matsalar sun yi nisa da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel