Gwamnonin APC 21 Sun Ki Amincewa da Wa’adin CBN Na Daina Amfani da Sabbin Naira

Gwamnonin APC 21 Sun Ki Amincewa da Wa’adin CBN Na Daina Amfani da Sabbin Naira

  • Gwamnonin jam’iyyar APC sun bayyana rashin amincewarsu ga wa’adin daina amfani da sabbin Naira
  • Ana kyautata zaton cewa, gwamnonin za su gana da Buhari don shaidawa masa abin da suke hangowa game da hakan
  • A baya El-Rufai ya ce, wannan sauyi na baktatan zai iya shafar siyasa da tattalin arzikin kasar nan

Najeriya - Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana kin amincewarsu ga wa’adin daina amfani da tsoffin kudi na 10 ga watan Fabrairu da CBN ta sanya, Daily Trust ta tattaro.

CBN ta ce za a daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 a Najeriya tare da ci gaba da amfani da sabbin da aka buga nan da 10 ga watan nan.

Sai dai, majiyoyi masu yawa sun bayyana cewa, gwamnonin kasar nan sun damu matuka da yadda ‘yan Najeriya ke shan wahalar neman sabbin kudaden da basu gama bazuwa cikin mutane ba.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Shugaban 'yan bindiga ya ce an yi aikin banza, ya samu buhun kudi ya siya makamai

Gwamnonin APC sun ki batun wa'adin CBN na 10 ga watan Fabrairu
Gwamnonin APC 21 Sun Ki Amincewa da Wa’adin CBN Na Daina Amfani da Sabbin Naira | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Daga nan ne aka ce gwamnonin suka yanke shawarin cewa, ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba tare da kara wa’adin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnoni za su gana da Buhari

Majiyoyin sun ce, gwamnonin za su gana da Buhari a yau Juma’a 3 ga watan Fabrairu da safe tare da bayyana masa manufarsu.

Daga cikin abin da za su bukata akwai fitar hanyar musayar kudi mai karfi ga mutanen kauye don tabbatar da sun rabu da tsoffin kudaden.

Sun kuma bayyana cewa, a halin yanzu CBN na kuntatawa ‘yan Najeriyan da basu ji ba basu gani ba ta fuskar tattalin arziki da tsaro a kasar.

Gwamnonin APC da abin da suka yanke

Idan baku manta ba, a cikin jihohi 36 na Najeriya, 21 dukkansu na APC ne mai mulkin kasa, wanda hakan ke da matukar tasiri ga shawari a kasar.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: El-Rufai ya tono batu, ya ce babu hankali a batun sauya fasalin Naira

Kafin su yanke shawarin ganawa da Buhari, gwamnonin na APC sun nada gwamnan Legas, Sanwo-Olu, na Kaduna El-Rufai, na Yobe Mai Mala Buni da na Ogun Dapo Abidon, inda suka gana da gwamnan CBN a ranar 30 da 31 na watan jiya.

A ganawar, sun bayyana rashin jin dadinsu da gaggawar da CBN ke yi na ganin an tabbatar da sabuwar dokar kudi baktatan ba tare da bata lokaci ba.

Kudi sun kare banki, CBN ya gaza karawa bankuna

Sun kuma shaidawa Godwin Emefiele, gwamnan CBN cewa, kudaden sun kare a hannun bankuna, kuma CBN ya gaza samar da kudaden ga bankunan don ba ‘yan Najeriya da ke cikin kunci.

Majiyoyin dai na bayyana cewa, gwamnonin na bukatar a kara wa’adin daina amfani da tsoffin kudi zuwa nan da watanni shida don kare siyasa da tattalin arzikin kasar.

Wannan ya yi daidai da abin da gwamna El-Rufai ya shaidawa BBC Hausa a wani bidiyon da kafar da ta yada a ranar Juma’a da safe.

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

Yayin da 'yan Najeriya ke kuka rashin sabbin Naira, wasu 'yan ta'adda sun bayyana -

Asali: Legit.ng

Online view pixel