Masu Garkuwa Da Mutane
Mataimakin shugaban kungiyar makiyayan Najeriya ta Miyyeti Allah (MACBAN) na kasa, Injiniya Munnir Atiku Lamido ya bata. Munnir na a hanyarsa ta zuwa Kaduna ne.
Masu garkuwa da mutane sun sako amarya mai suna Rukkayat Musa da ƙannen mijinta mata guda biyu da suka sace a jihar Kwara. An biya N7m a matsayin kuɗin fansa.
Wanda ake da zargi da garkuwa da wata budurwa mai suna Ese Oruru daga Bayelsa zuwa Kano, Yunusa Yellow ya shaki iskar 'yanci bayan kammala zaman gidan kaso.
Ƴan bindiga sun addabi yankin ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi. Ƴam bindigan sun yi garkuwa da mutum huɗu a hare-haren da suka kai ƙauyukan da ke a yankin.
'Yan bindiga sun sace wata manajar bankin Sterling Mai suna Nneka Unoka a jihar Bayelsa yayin da take kan hanyarta na zuwa wurin aiki a cikin birnin Yenagoa.
Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake Shedrack Durojaiye Obibeni, da mai ɗakinsa a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas da ke jihar Kogi, da yammacin ranar Litinin.
Babban malamin addinin musulunci, Ibrahim Oyinlade, wanda masu garkuwa da mutane suka sace a ƙauyen Uso jihar Ondo, ya kuɓuta daga hannun miyagun a ranar Lahadi
Miyagun sun je gidan Basarake sun bindige shi, sun bi daki-daki, sun kashe ‘ya‘yansa. Ardon birnin Zazzau da kewaye ya na barzahu a dalilin ta’adin ‘yan bindiga
'Yan bindiga a dajin Kagarko da ke jihar Kaduna sun harbe kafar wani da ya yi kokarin guduwa daga komarsu mai suna Ifeanyi a karamar hukumar Kagara ta jihar.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari