Tsohon Ministan Buhari Ya Fallasa Ainihin Mutanen da ke Jawo Rashin Tsaro a Najeriya

Tsohon Ministan Buhari Ya Fallasa Ainihin Mutanen da ke Jawo Rashin Tsaro a Najeriya

  • Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya gabatar da jawabi a kan batun tsaro da shirin zabe
  • Tsohon Ministan harkokin cikin gidan yana zargin ‘yan siyasa da laifin matsalolin da ake samu
  • Da yake jawabi a taron, an fahimci Dambazau yana ganin jami’an tsaro sun yi wa zaben 2023 tanadi

Abuja - Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya zargi ‘yan siyasa da hannu a matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a bangarorin kasar nan.

Abdulrahman Dambazau ya halarci wani taro da kungiyar 'I Am Change' ta shirya a garin Abuja. The Cable ta ce ya gabatar da jawabi kan inda ya kware.

Taron da aka yi ranar Alhamis a dakin taro na ‘Yaradua ya tabo lamarin barazanar tsaro yayin da ake shirin gudanar da babban zabe nan da ‘yan kwanaki.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga Sun Shiga Gida, Sun yi Nasarar Awon Gaba da Hakimi a Arewacin Najeriya

Tsohon shugaban hafsun sojan kasar ya shaida cewa jami’an tsaro sun yi bakin kokarinsu a wajen magance matsalolin rashin tsaro a zabe mai zuwa.

Babu zabe inda babu jami'an tsaro

Janar Abdulrahman Dambazau (rtd) yake cewa sai da jami’an tsaro za a iya shirya zabe na kwarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto tsohon Ministan harkokin cikin gidan yana cewa an kawo rashin zaman lafiya a dalilin irin kazamar siyasar da aka bijiro da ita a halin yanzu.

Abdulrahman Dambazau
Abdulrahman Dambazau Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Maganar Janar Abdulrahman Dambazau (rtd)

“Mai girma shugaban kasa ya fada sau da-dama cewa yana so a yi zaben adalci na gaskiya, kuma ba za mu iya zaben kwarai ba tare da cikakken tsaro ba.
Shekarun baya, hankalinmu yana kan Arewa maso gabas, yanzu mun koma kan Kudu maso gabas da inda da ake garkuwa da mutane da rikicin makiyaya

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro Ya Fatattaki ‘Dan Takaran Shugaban kasa, Ya Hana Shi Taro a Katsina

Musamman a Kudu maso gabas, inda haramtaciyyar kungiyar IPOB ta rantse ba za ayi zabe ba.
Saboda haka, irin kalubalen da nake magana kenan, kuma na tabbata cewa hukumomin tsaro sun yi bakin kokarinsu wajen ganin sun magance lamarin.

- Abdulrahman Dambazau

Inda 'yan siyasa suka shigo

‘Yan siyasa da kansu suka kirkiri wasu daga cikin kalubalen tsaron nan saboda ana siyasar kabilanci, siyasar addini, da kuma siyasar bangaranci.
Wadannan ke raba kan jama’a, su jawo tashin-tashina. Ina ganin ya kamata ‘yan siyasa su nuna kishin kasa, su yi abin da ya fi dacewa da kasar nan."

- Abdulrahman Dambazau

Za a hana su biza - Amurka

Kun samu rahoto cewa a birnin Washington DC da ke Kasar Amurka ta ce samun takardar biza za ta gagari masu shirin magudi da murde zabe a 2023.

Sakataren Gwamnatin Amurka, Antony Blinken ya bada sanarwar nan, ya nuna su na kokarin wanzar da tsarin damukaradiyya da yakar rashin bin doka.

Kara karanta wannan

'Kana Bukatar Taimako', Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Kalaman Tanko Yakasai Kan Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel