Kafin a je ko ina, ‘Yan Bindiga Sun Tara Buhunan Sababbin Nairorin Sayen Makamai

Kafin a je ko ina, ‘Yan Bindiga Sun Tara Buhunan Sababbin Nairorin Sayen Makamai

  • A halin yanzu mutanen Najeriya na wahala saboda matukar karancin sababbin kudin da aka buga
  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da wasu takardun kudi domin inganta tsaro da tattalin arziki
  • Ana wannan sai ga shi ‘yan bindiga sun fitar da bidiyo, su na fadar cewa sababbin kudin sun zo masu

Nigeria - A wani faifen bidiyo da aka fitar, an fahimci an samu wasu ‘yan bindiga da suke da’awar har sababbin kudin da aka buga sun shigo hannunsu.

A wani rahoto da aka fitar a Aminiya, miyagun ‘yan bindigan sun ce sun cigaba da aika-aikarsu domin har sun mallaki takardun kudin da aka fito da su.

A wannan bidiyo, za a ji ‘yan bindigan su na cewa wasu wadanda aka tanadi kudin dominsu ba su sa hannu a kan su ba, amma tuni har sun mallake su.

Kara karanta wannan

Mun San Abin da Muka Gani: Dalilin Hana Masoyan Tinubu Yin Gangami Inji ‘Yan Sanda

An rahoto wannan ‘dan bindiga yana cika-bakin sun tara sababbin kudi makil, ya ce Allah (SWT) kadai ne ya san iyakar adadin buhunan da suke da su.

Idan dai abin da suke fada gaskiya ne, ‘yan bindigan sun ce akwai wani Bawan Allah da suka yi garkuwa da shi wanda shi da bai da sababbin Nairorin.

Ina da N10m a gida - 'Dan bindiga

‘Dan bindigan ya tabbatar da sun yi amfani da sababbin takardun kudin wajen sayen makamai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan Bindiga
Wani jejin da 'Yan bindiga suke Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Yayin da kakakinsu yake tunkahon, sai aka ji wani a gefe guda yana cewa yana da Naira miliyan 10 na kudin da CBN ya buga, ya ce su na ajiye a gida.

Anya kuwa?

Sai dai Legit.ng Hausa ta na shakkar gaskiyar lamarin, musamman ikirarin cewa akwai wanda ya ke da miliyoyin sababbin kudin a daidai lokacin nan.

Kara karanta wannan

Sabon salo: 'Yan jihar Arewa sun koma amfani da kudin wata kasa a madadin Naira

Jaridar da ta kawo rahoton ba ta tabbatar da ingancin wannan bidiyo da ‘yan bindigan suka fitar ba. Zuwa yanzu hukuma ba ta ce komai ba a kai.

Daga cikin dalilan da suka jawo Gwamnan babban bankin Najeriya ya canza manyan kudi na N200, N500 da N1000, akwai kokarin magance rashin tsaro.

CBN ya ce akwai ‘yan bindiga da ke daji da suka tara kudin fansa, a dalilin haka aka canza kudi saboda a lalata wannan danyen aikin da miyagu suke yi.

Barayi a shagon POS

A farkon makon muka samu labarin yadda ‘Yan fashi su ka shiga shagon POS su na neman sabon kudi, suka yi ta harbe-harbe, kuma suka sace N7m.

‘Yan Sanda sun ce za a cigaba da bakin kokari wajen cafke wadanda suka yi wannan danyen aikin. Abin ya faru a karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel