Zababben ‘Dan Majalisa Ya Sha da Kyar, An Kusa Kashe Shi, An Kona Motarsa Kurmus

Zababben ‘Dan Majalisa Ya Sha da Kyar, An Kusa Kashe Shi, An Kona Motarsa Kurmus

  • Aondona Dajoh bai gama murnar cin zabe ba, wasu miyagu suka auka masa, za su ga bayan shi
  • Zababben ‘dan majalisar ya sha da kyar ne a sakamakon harin da aka kai masa a Gyado a Benuwai
  • Nan da watan Yuni za a rantsar da Dojah a matsayin ‘dan majalisar dokoki mai wakiltar Gboko

Benue - Aondona Dajoh wanda ya yi nasarar lashe zaben ‘dan majalisa mai wakiltar Gboko ta yamma a jihar Benuwai ya tsira da ransa da kyar.

The Sun ta kawo rahoto a ranar Juma’a cewa wasu miyagu sun yi nufin kashe Aondona Dajoh, sun auka masa yayin da yake tafiya a mota.

Wadannan miyagu da ba a san su ba, sun shirya masa kwantan-bauna a hanyarsa ta zuwa gida a daren Juma’a, saura kiris a hallaka 'dan siyasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Daba Sun Tare Zababben Dan Majalisa A Arewa, Sun Cinnawa Motarsa Wuta

Ko da zababben ‘dan majalisar Gboko ta yamma a majalisar dokokin Benuwai ya sha da kyar, motar da yake ciki ta kone kurmus, ta zama toka.

An rutsa Honarabul a Gyado

Tribune ta ce an aukawa wannan Bawan Allah ne a daidai yankin Gyado da ke karamar hukumar Gboko da yammacin ranar Alhamis da ta gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta ce dole ‘dan majalisar mai jiran gado ya rabu da motarsa, ya ari ta kare yayin da ya tabbatar da wadannan mutane za su ga bayan shi.

Benuwai
Wani titi a Benuwai Hoto: Getty
Asali: Getty Images

'Yan sanda sun yi magana

Da manema labarai suka tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar wannan lamari a jiya.

SP Catherine Anene ta ce babu shakka an kai wa Hon. Aondona Dajoh, duk da ya tsere ba tare da ko da rauni a jikinsa ba, amma an kona abin hawansa.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Anene ta sakon wayar salula, ta bayyana cewa Jami’an tsaro sun fara bincike a kan batun da nufin gano wadanda suka yi aika-aikan, sai a hukunta su.

A makon jiya aka yi zaben jihohi, Dajoh da ire-irensa suka lashe kujerun majalisar dokoki.

Barazanar Shema a PDP

A gefe guda, an ji labari Ibrahim Shehu Shema wanda bai taba barin Jam’iyyar PDP ba, yana tunanin ya sauya-sheka bayan dakatar da shi da aka yi.

Tsohon Gwamnan Katsina wanda yana cikin majalisar NEC da BOT ya ba NWC kwanaki ta dawo da shugabannin reshen Katsina da NWC ta sauke su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel