Abun Takaici: Halin Ƙuncin Da Ɗaliban Da Ƴan Bindiga Suka Sace Suke Ciki

Abun Takaici: Halin Ƙuncin Da Ɗaliban Da Ƴan Bindiga Suka Sace Suke Ciki

  • Satar ɗaliban makaranta a makarantun gwamnatin Najeriya ya fara zama ruwan dare a ƙasar
  • Ƴan bindiga a lokuta da dama sun sha zuwa makarantun kwana suna tafiya da ɗalibai domin a basu kuɗin fansa
  • Waɗannan ɗaliban suna rayuwar ƙunci da takaici a hannun ƴan bindigan inda suke aurar da wasu mata daga cikin su

Ɗaliban makarantar sakandiren gwamnatin tarayya ta FGC Birnin-Yauri a jihar Kebbi, ba za su taɓa mantawa da ranar 17 ga watan Yunin 2021 ba.

Wannan ranar ta 17 ga watan Yunin 2021 rana ce ta baƙin ciki, takaici da tashin hankali wanda ya gusar da duk wani ɓurɓushin farin cikin da suke da shi a rayuwar su, rahoton HumAngle.

A wannan ranar ne dai ƴan bindiga suka yiwa makarantar ƙawanya suka sace ɗalibai maza da mata, suka wuce da su cikin daji.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ta Sake Ɓarkewa Kan Karancin Kuɗi, An Cinnawa Bankuna Wuta

Yauri
Abun Takaici: Halin Ƙuncin Da Ɗaliban Da Ƴan Bindiga Suka Sace Suke Ciki
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Yan Bindigan suka dira makarantar

Ƴan bindigan sun isa makarantar ne dai da wajen ƙarfe sha biyu na dare akan babura, inda suka kama harbe-harben bindigogi, sun buɗewa masu gadin dake gadi a lokacin wuta bayan sun ƙi buɗe musu ƙofar shiga makarantar.

Ƴan bindigan waɗanda yaran ƙasurgumin ɗan bindigan nan ne Dogo Gide, a wannan ranar bayan sun gama cin karen su babu babbaka, sun kuma sace ɗalibai 112 tare da malamai 8 inda suka tafi da su cikin daji.

Bayan sun kwashe tsawon watanni a hannun ƴan bindigan cikin daji, an fara sako wasu daga cikin su.

A watan Oktoban 2021 an sako ɗalibai 30 daga cikin su, yayin da aka sako ragowar ɗaliban a ranar 8 ga watan Janairun 2022.

Sai dai wani abun ban takaici shine Dogo Gide ya riƙe ɗalibai mata guda 11 daga cikin su inda yayi musu auren dole.

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: Marasa Lafiya Na Shan Wuya, Magani Yayi Musu Wahalar Samu, Kungiyar Likitoci

Dalibai 14 dake hannun yan bindigan har yanzu

A cewar bayanin da jaridar The Cable ta samu daga hannun iyayen yaran waɗanda suka amince a wallafa sunan yaran, sunayen ɗalibai matan da suke a hannun ƴan bindigan sune Farida Ka’oje, Hafsa Murtala, Rebecca James, Bilhah Musa, da Rahman Abdullahi.

Sauran sun haɗa da Esther Sunday, Faiza Ahmed, Aliya Abubakar, Neempere Daniel, Elizabeth Ogechi Nwafor, da Safiya Idris. Dukkan su suna a tsakanin shekara 13 zuwa 16 a duniya lokaci. da ka sace su a 2021.

Haka kuma Gide ya riƙe wani yaro mai suna Safiyanu Idris, wanda aka ce ya mayar da shi bawa.

Dogo Gide ya aura ma kan shi ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Farida, inda akayi bikin a gaban ɗaliban da malaman su, wanda yaran da aka aurar ɗin suka yi ta kukan baƙin ciki.

"A lokuta da dama za su kira yaran ciki su kwanta da su," A cewar wani ɗalibi Garba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari

"Wasu lokutan za su sanya ɗalibai maza su kwanta da ɗalibai mata a gaban kowa domin kawai su yi nishaɗi."
“Ranar da Dogo Gide ya auri Farida, ya biya sadakin ta ga malamin mu Bashir. An raba mana tsokar nama. Sauran yaran an aurar da su ga ƴan bindiga sannan kowacce an bata sadakinta. Har yara ƴan JSS 1 suka aurar."
"Yaran sun yi ta sharɓar kuka amma basu samu ɗauki ba. Ɗaya daga cikin su tayi ƙoƙarin guduwa amma ƴan bindigan sun kamo ta sannan suka yi mata shegen duka."

Iyayen yaran sun shiga damuwa da baƙin ciki lokacin da suka ji labarin cewa an aurar da ƴaƴan su.

Bukatar Dogo Gide

Dogo Gide dai ya nemi da a bashi naira miliyan ɗari da sabbin babura 30 a matsayin kuɗin fansa kafin ya sako ragowar ɗaliban mata.

Ƙungiyar YEDA ta rubuta wasiƙu ga gwamnatin jihar, gwamnatin tarayya, majalisar wakilai, kan buƙatar a ceto yaran, amma har yanzu basu cewa ƙungiyar komai ba.

Kara karanta wannan

2023: Bai San Mu Bamu San Shi Ba, Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Nesanta Kanta Da Takarar Atiku

Yanzu haka iyayen yaran yaran sun haɗa ƙungiya domin tara kuɗin fansar, amma Dogo Gide yace baya son kuɗin su, so yake gwamnati ta biya.

Ya zuwa yanzu dai sun samu sun tara naira miliyan 48.

Wannan satar ɗaliban dai ba ƙaramin koma baya bane ga harkar ilmi a yankin Arewacin Najeriya, inda ake da yawan yara waɗanda basu zuwa makaranta.

Girgizar Kasar Turkiyya-Syria: Sama da Mutum 44,000 Sun Rasa Rayukansu

A wani labarin na daban kuma, an bayyana adadin yawan mutane da suka rigamu gidan gaskiya a iftila'in girgizar ƙasar da ya auku a ƙasashen Turkiyya da Syria.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da mutum dubu arba'in da huɗu ne suka rasu a dalilin girgizar ƙasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel