Yan Sanda Sun Cafke Wata Mata Mai Safarar Makamai Ga Ƴan Bindiga

Yan Sanda Sun Cafke Wata Mata Mai Safarar Makamai Ga Ƴan Bindiga

  • Hukumar ƴan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar yin wani babban kamun wata ɓata gari
  • Hukumar ta samo nasarar cafke wata mata mai safarar makamai ga ƴan bindigan da suka addabi jihar
  • Matar ta bayyana cewa ta daɗe a cikin wannan baƙar sana'a ta safarar makamai ga ƴan bindiga

Hukumar ƴan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa jami'anta sun cafke wata mata mai safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar.

Hukumar ƴan sandan tace ta cafke matar mai suna Fatima Sani, bisa zargin ta da hannu wajen safarar makamai ga wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar. Rahoton The Cable

Yan bindiga
Yan Sanda Sun Cafke Wata Mata Mai Safarar Makamai Ga Ƴan Bindiga
Asali: UGC

Da yake magana da ƴan jarida a ranar Juma'a, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, yace an cafke wacce ake zargin ne bayan an samu bayanai kan laifukan da take aikatawa.

Kara karanta wannan

"Mu ƴan APC ne, Amma PDP Zamu Zazzagawa Kuri'un Mu a Zaɓen Gwabna": Jigon APC a Nasarawa

“A ranar 13 ga watan Fabrairun 2023, jami'an ƴan sanda sun cafke Fatima Sani ɗauke da harsasai guda 325, bayan an samu bayanin cewa tana ɗauke da kayan daga Lafia na jihar Nasarawa domin kai wa wani ƙasurgumin ɗan bindiga dake ɓoye a dajin Zamfara." A cewar sa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yayin da take amsa tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ta daɗe a cikin wannan baƙar harkar, sannan ta taɓa kawo harsasai guda dubu ɗaya na bindigar AK-47 da bindigu guda uku ƙirar AK-47 ga ƴan bindiga a jihar Zamfara."

Haka kuma ƴan sandan jihar sun cafke wasu masu garkuwa da mutane ciki har da wanda ya kitsa yadda aka sace mahaifiyar sa. Rahoton TVC News

Muhammad Shehu ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a tura wacce ake zargin zuwa gaban kotu.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mayaƙan Boko Haram Tsagin ISWAP Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno

Ana Dab Da Fara Zaɓe a Najeriya, Majalisar Ɗinkin Duniya Tace Akwai Damuwa

A wani labarin na daban kuma, majalisar ɗinkin duniya ta nuna shakku kan yiwuwar gudanar da zaɓen dake tafe a Najeriya.

Majalisar ɗinkin duniyan ta bayyana fargabar da take yi ne ta hannun kodinetan ta na Najeriya Mathias Schamale.

Hukumar ta zayyano wasu abubuwa guda huɗu waɗanda suka sanya ta shiga kokwanto kan yiwuwar gudanar da zaɓe a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel