Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa

Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa

  • Rundunar yan sandan Zamfara ta yi nasarar kama gungun masu garkuwa da mutane biyo bayan wasu bayanan sirri
  • Daya daga cikin masu garkuwar, Thomas Yau, ya bayyana yadda aka hada kai da shi aka yi garkuwa da mahaifiyarsa tare da karbar kudin fansa
  • Rundunar yan sanda ta ce da zarar ta kammala bincike za ta mika wanda ake zargi kotu don girbar abin da suka shuka

Zamfara - Rundunar yan sanda ta Jihar Zamfara ta tsare wani yaro mai shekara 20 bisa zargin hada kai da wasu mutane biyar don yin garkuwa da mahaifiyarsa da wasu mutum uku tare da karbar kudin fansa naira miliyan 30, rahoton The Punch.

Kakakin yan sandan Jihar, SP Mohammed Shehu, da ya ke shaidawa yan jarida yadda lamarin ya faru a Gusau, babban birnin jihar, ranar Juma'a, 17 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

Yan sanda
Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wanda ake zargin, Thomas Ya'u, ya sanarwa yan sanda cewa kowanne daya daga cikin wanda aka yi garkuwar da su ya biya Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa, ciki hadda mahaifiyarsa, jimillar naira miliyan 30.

Shehu ya ce:

''A ranar 12 ga Fabrairu, 2023, rundunar yan sandan Jihar Zamfara, ta hannun wakilanta na cikin mutane, tayi aiki da wasu bayanan sirri da yayi silar gano maboyar masu garkuwa tare da kama shida daga ciki, wanda suka fitini kauyuka daban-daban a Kaduna, Kano da sauran makwabtan jihohi, kamar Zamfara da Sokoto.
''Bayan gudanar da bincike, an gano yadda masu garkuwar suka dinga aikata garkuwar, inda suka yi garkuwa da mutanen da ba a san adadin su ba tare da karbar miliyoyi a matsayin kudin fansa.
''Kowanne daga cikin Wanda ake zargin ya bayyana adadin garkuwar da yayi, da kuma irin rawar da ya taka."

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Ya cigaba da cewa:

''Abin mamaki, daya daga cikin wanda ake zargin, Thomas Ya'u, ya shaida cewa wani lokaci a shekarar da ta gabata, ya shirya yadda aka yi garkuwa da mahaifiyarsa da wasu mutane.
''Sun karbi Naira miliyan 30 daga yan uwan su a matsayin kudin fansa, inda shi kuma, aka bashi miliyan guda a matsayin kason shi.''

Shehu ya tabbatar da cewa ana kan gudanar da bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala.

Wani ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi kudin fansa N2.5m

A wani rahoton kun ji cewa wani mata matashi, Issa Naigheti ya shiga hannun yan sanda kan zarginsa da garkuwa da mahaifinsa.

Ajayi Okasanmi, kakakin yan sandan jihar ya sanar da hakan, ya ce an kama matashin a garin Kambi da ke Ilorin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel