Masu Garkuwa Da Mutane
Yan bindiga sun saki bidiyon 'yan mata 63, ciki har da wata amarya, kawayenta da 'yan uwanta da suka sace a karamar hukumar Sabuwa, jihar Katsina.
An bukaci Gwamnatin Tinubu ta aiwatar da manufofin APC. ‘Dan takaran shugaban kasar a zaben 2019 yana so gwamnatin Bola Tinubu tayi wa tsarin mulki kwaskwarima
Yan sanda sun yi nasarar damke mutum shida, maza huɗu da mata biyu, bisa zargin garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja, sun kwato makamai da kayayyaki.
An yi garkuwa da wasu matafiya daga Umuahia na jihar Abia a cikin wasu manyan motocin alfarma guda biyu a karamar hukumar Olalamaboro ta jihar Kogi.
Oba Adebayo Fatoba, babban basarake a jihar Ekiti, ya bayyana yadda ya tsira daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka halaka takwarorinsa biyu.
Daya daga tsoffin shugabannin hukumar DSS ya bayyana yadda ya ga abin da ya gani a wurin 'yan bindiga. Ya ce ya daina sukar masu biyan kudin fansa a yanzu.
Masu garkuwa da mutanen da suka sace mutane a yankin Bwari dake babban birnin tarayya sun bukaci a kawo masu babura biyu bayan sun karbi kudin fansa miliyan 8.5.
'Yan bindigar da suka yi awon gaba da daliban makaranta a jihar Ekiti sun rage kudin fansarsu zuwa naira miliyan 15.Sun yi barazanar kashe su idan ba a biya ba.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami'anta sun yi nasarar ceto mutum uku daga hannun ƴan bindiga bayan musayar wuta a jihar Taraba ranar Talata.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari