‘Yan Bindigan da Suka Sace ‘Yan Makarantar Ekiti Sun Yi Barazanar Kashe Su

‘Yan Bindigan da Suka Sace ‘Yan Makarantar Ekiti Sun Yi Barazanar Kashe Su

  • 'Yan bindigan da suka sace daliban makaranta a Ekiti sun rage kudin fansarsu daga naira miliyan 100 zuwa miliyan 15
  • Maharan sun bukaci yan uwansu da su gaggauta biyan kudin fansa domin a cewarsu yaran sun fara galabaita
  • Haka kuma, sun yi barazanar sheke su idan har ba a biya kudin fansar da suka rage ba cikin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Masu garkuwa da mutanen da suka sace 'yan makaranta biyar da ma'aikatan makarantar Apostolic Faith Group hudu, Emure Ekiti, sun yi barazanar kashe su idan iyayensu suka ki biyan kudin fansa cikin gaggawa.

'Yan uwan wadanda aka sacen sun bayyana a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairu, cewa masu garkuwa da mutanen sun rage kudin fansar zuwa naira miliyan 15, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

Yan bindiga sun yi barazanar kashe yaran makarantar Ekiti
‘Yan Bindigan da Suka Sace ‘Yan Makarantar Ekiti Sun Yi Barazanar Kashe Su Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan sanda suka ce sun kama mutum 13 da hannu a kisan sarakuna biyu a Ekiti, Onimojo na Imojo, Oba Olatunde Olusola da Elesun na Esun Ekiti, Oba Babatunde Ogunsakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga da ke kaddamar da hare-harensu a hanyar Emure-Ekiti — Iporo Ekiti sun farmaki wata motar bas dauke da dalibai kimanin su 25 bayan an tashi makaranta.

'Yan bindiga sun yi barazanar kashe yaran - Inji iyayensu

A hira mabanbanta da aka yi da su, 'yan uwan wadanda aka sace sun bayyana cewa maharan, wadanda suka bukaci a biya naira miliyan 100 a baya sun rage zuwa naira miliyan 15 bayan an tattauna da su.

Sai dai kuma, yan uwan sun ce masu garkuwa da mutanen sun dage lallai a biya kudin da suka rage akan lokaci, suna masu gargadin cewa yaran da suka sace sun fara galabaita, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sake hana bada kudin fansa idan an yi garkuwa da mutane a Najeriya

A cewarsu kuma, sun kuma yi barazanar kashe mutanen da ke hannun nasu, idan 'yan uwansu suka ki biyan kudin fansarsu.

Jawabin shugabar makarantar da aka sace dalibai

Da farko dai mun ji cewa shugabar makarantar da ke garin Ekiti, Boje Olanireti ta shaida cewa 'yan bindigar sun nemi a biya N100m da ta zanta da jaridar Punch a yammacin ranar da abin ya faru.

Boje Olanireti ta ce an tare motar ne kimanin mintuna biyar da barinsu makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel