Shahararren Malamin Addini Ya Tona Asirin Malaman da Ke Kara Rashin Tsaro a Kasar, Ya Ba da Shawara

Shahararren Malamin Addini Ya Tona Asirin Malaman da Ke Kara Rashin Tsaro a Kasar, Ya Ba da Shawara

  • Shahararren Fasto a Najeriya, Oscar Amechina ya fadi yadda malaman addini ke taimakawa wurin kara rashin tsaro a kasar
  • Faston ya ce mafi yawansu su na wa’azi ne don neman kudi da kuma suna madadin koyar da dabi’u masu kyau
  • Amaechina wanda shi ne shugaban cocin African Mission ya bayyana haka yayin kaddamar da wani littafi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Firaccen Fasto a Najeriya, Oscar Amaechina ya bayyana yadda malaman addini ke taimakawa rashin tsaro.

Oscar ya ce mafi yawan Fastoci suna wa’azi ne don neman suna da kuma kudi madadin koyar da dabi’u masu kyau, cewar Leadership.

Malamin addini ya fadi masu kara rashin tsaro a Najeriya
Fasto ya bayyana irin malaman da ke kara rashin tsaro a Najeriya. Hoto: Oscar Amaechina.
Asali: Facebook

Mene Faston ke cewa kan rashin tsaro?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kwankwaso ya yi martani kan matakin Tinubu na fitar da abinci, ya roki jama'a

Faston ya ce hakan ya na tasiri wurin kara matsalar rashin tsaro a kasar inda ya shawarce su da su tsaya kan kowaryar littafi mai tsarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaechina wanda shi ne shugaban cocin African Mission and Evangelism Network ya bayyana haka yayin kaddamar da wani littafi a Abuja.

Ya shawarci Fastoci da su tsaya ga koyarwar littafi mai tsarki ga mambobinsu da kuma rage musu son duniya, cewar Premium Times.

Shawarar da Faston ya bayar

A cewarsa:

“Matsalar koyarwa don neman suna da abin duniya kawai kara rashin tarbiya yake tsakanin al’umma.
“Na yi matukar imani cewa hakan babu abin da ya ke karawa sai rashin tsaro ganin yadda muke gudanar da rayuwarmu babu ubangiji.
“Duk lokacin da ka kalli kalubalen da muke da su a Najeriya, rashin tsaro shi ne babban abin da ya addabe mu.”

Kara karanta wannan

Ministocinsa 2 sun je Majalisa, sun soki tsari da manufofin Gwamnatin Bola Tinubu

Ya ce mafi yawan masu garkuwa su na da addininsu da suke bauta, wasu su na zuwa coci kuma su na ba da kudin baiko ga Fastoci a coci.

Oscar ya ce wasu daga cikinsu har gina coci-coci suke yi saboda rashin tarbiyar addini inda ya ce idan kasan ubangiji za ka bi shi da dokokinsa.

Malamin addini ya yi hasashen wasan Najeriya

Kun ji cewa, Fasto Kan Ebube ya yi hasashen kasar da lashe wasan da za a gudanar a gobe a gasar AFCON da ake a Ivory Coast.

Ebube ya ce kasa mai masaukin baki ce za ta lashe kofin amma da kuskuren alkalan wasan da za su hura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel