Ina Sukar Biyan da Kudin Fansa a Baya, Sai da Aka Sace Ni Na Gane, Tsohon Shugaban DSS Ya Magantu

Ina Sukar Biyan da Kudin Fansa a Baya, Sai da Aka Sace Ni Na Gane, Tsohon Shugaban DSS Ya Magantu

  • Mike Ejiofor, daya daga cikin tsoffin shugabannin DSS ya ce, a baya yana sukar iyalan da ke biyan kudin fansa, har sai da ya shiga hannun ‘yan bindiga
  • Ejiofor ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da satar mutane ya zama ruwan dare a Najeriya kana gwamnati ta gaza shawo kan lamarin
  • Ya fadi hakan ne a lokacin da yake martani ga sace wasu masu sarautar gargajiya da aka sace a Ekiti da Kwara da kuma satar da addabi ‘yan Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Wani tsohon daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Mike Ejiofor, ya ce yakan soki biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga har sai da aka yi garkuwa da shi a kwanan baya.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Ejiofor ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Vanguard, wanda aka buga a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu.

Ejiofor ya bayyana cewa a ko da yaushe gwamnati kan hana mutane biyan kudin fansa, ya kara da cewa amma mutane na kare kansu idan gwamnati ta gaza ceto su ta hanyar biyan fansan.

Tsohon shugaban DSS ya fadi magana mai tada hankali kan biyan kudin fansa
Bana goyon bayan fansa, amma na gani da ido na | Hoto: @Naija_PR
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meye yasa Ejiofor ke fadin haka?

A cewarsa:

"Kafin a sace ni, na sha cewa mutane bai kamata suke biyan kudin fansa ba. Amma wannan tunanin ya canza bayan da aka taba sace ni, wanda ya ji ya san haka. Sai dai idan ba a rutsa da kai ba, za ka yi duk mai yiwuwa ciki har da biyan kudin fansa a saki danginka."

Legit.ng ta ruwaito cewa, sama da shekaru 10 yanzu kenan kungiyoyin ‘yan ta’adda na addabar ‘yan Najeriya da sace-sace da hare-haren ta’addanci.

Kara karanta wannan

Bai kamata a fara sukar gwamnatin Tinubu ba daga yanzu, Shehu Sani ya bayyana dalili

Hakan ya kai ga asarar dukiya da rayukan da basu ji ba basu gani ba a yankuna daban-daban na kasar mai yawan jama’a.

Wane irin asara Najeriya ta yi na rayuwa da dukiya?

A lokuta da dama, sukan kashe mutane ko kuma su nemi fansan miliyoyin kudaden da mutane da yawa ba za su iya biya ba ko kuma basu da hanyarsa.

A wasu lokuta, an kashe wanda aka kashe bayan danginsa sun kasa tara kudin fansa.

Tsakanin shekarar 2014 zuwa 2020, an yi ta samun yawaitar sace-sacen ‘yan makaranta a Najeriya, ciki har da sace ‘yan matan makarantar Chibok da ya dauki hankulan duniya.

Kadan daga rahotannin ta’addanci a Najeriya:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

'Yan bindiga sun sace malamin jami'a

A wani labarin, wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da malamin jami'ar kimiyya da fasaha da ke Alieru, jihar Kebbi, Dakta Musa Sale Argungu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lakcaran da 'yan bindigan suka sace shi ne mataimakin shugaban "Faculty of Physical Sciences" na jami'ar.

Shugaban kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) reshen jihar Kebbi, Dakta Abubakar Birnin Yauri, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce an sace malamin da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel