Babban Basarake Ya Bayyana Yadda Ya Tsira Daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

Babban Basarake Ya Bayyana Yadda Ya Tsira Daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

  • Oba Adebayo Fatoba ya ce ikon Allah ne ya kuɓutar da shi daga mummunan harin da masu garkuwa da mutane suka kai musu ba tsafi ba
  • Duk da cewa Oba Fatoba ya amince cewa harsashin maharan ya kasa ratsa jikinsa, Sarkin na Ekiti ya nuna baƙin cikinsa kan takwarorinsa da suka rasa ransu
  • Oba Fatoba ya bayyana cewa maharan na ɗauke da manyan muggan makamai lokacin da suka kai musu hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ado-Ekiti, jihar Ekiti - Alara na Ara-Ekiti a ƙaramar hukumar Ikole ta jihar Ekiti, Oba Adebayo Fatoba, ya bayyana yadda ya yi nasarar tserewa daga harin da ƴan bindiga suka kai kwanan nan.

Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga watan Janairu, ƴan bindiga sun kashe wasu sarakunan gargajiya a Ekiti guda biyu, Onimojo na Imojo, Oba Olatunde Olusola da Elesun na Esun Ekiti, Oba Babatunde Ogunsakin.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fadi babban dalili 1 da ya sa ya dakatar da fitaccen basarake a jiharsa

Basaraken Ekiti ya magantu kan kubuta daga hannun 'yan bindiga
An halaka sarakunan gargajiya biyu a Ekiti kwanan nan Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

"Ban ɓace ba': Oba Fatoba

Oba Fatoba ya bayyana cewa bai yi layar zana daga wurin da lamarin ya faru ba kamar yadda wasu ke hasashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Awikonko kan abin da ya faru a wani faifan bidiyo, Fatoba ya bayyana cewa ikon Allah ne kawai ya sa ba a kashe shi ba.

A kalamansa:

“Muna tattaunawa ne kan yadda marigayi Onimojo, mataimakin farfesa ke shirin baro jami’ar fasaha ta tarayya da ke Akure (FUTA) zuwa jami’ar tarayya da ke Oye-Ekiti (FUOYE) a kan hanyar Irele a lokacin da maharan suka ritsa mu.
"Ba mu taɓa sanin suna da yawa ba saboda mutum uku daga cikinsu sun nuna mana bindigogi. Mun yi kokarin yin kokawa da su amma sai suka fara harbinmu ta ɓangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

FAAN: Ministan Tinubu ya bayyana alfanun da za a samu kan mayar da ofishin Legas, ya fadi dalili

"Duk da cewa harsasan ba su shiga ba, amma na gane cewa suna ɗauke da muggan makamai. Mun gudu daga wurin zuwa wani shingen bincike da mafarautanmu na yankin suka sanya.
"Amma ganin bindigogi da ke hannun masu garkuwa da mutanen, mafarautan sun kasa fuskantarsu. Har ma na nemi ɗaya daga cikin mafarautan ya mayar da wuta amma bindigarsa ta kasa aiki. A lokacin da na waiwaya, sai na ga gawarwakin sauran sarakunan kwance cikin jini."

Ɗaliban Ekiti Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗalibai da malaman makarantan da aka sace a jihar Ekiti sun shaƙi iskar ƴanci.

Mutanen dai sun kuɓuta daga hannun ƴan bindigan ne bayan sun kwashe kwana bakwai suna tsare a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel