Katsina: Yan Bindigar da Suka Sace Amarya Da ’Yan Mata 63 Sun Saki Sabon Bidiyo, Sun Gargadi Gwamna

Katsina: Yan Bindigar da Suka Sace Amarya Da ’Yan Mata 63 Sun Saki Sabon Bidiyo, Sun Gargadi Gwamna

  • Kasa da mako daya da sace 'yan matan amarya 63 a jihar Katsina, 'yan bindiga sun saki sabon bidiyo wanda ya nuna halin da suke ciki
  • A cikin bidiyon, an ga jerin 'yan matan, inda wani ɗan bindiga ke barazanar za su sake aurar da amaryar idan ba a biya kudin fansa ba
  • Wani mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin Katsina, ya ba gwamna Dikko Radda shawarar hanyar kwato 'yan matan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Yan bindiga sun saki bidiyon 'yan mata 63, ciki har da wata amarya, kawayenta da 'yan uwanta da suka sace a karamar hukumar Sabuwa, jihar Katsina.

A cikin bidiyon, 'yan bindigar sun yi barazanar za su sake yi wa amaryar wani sabon aure idan har ba a biya kudin fansar 'yan matan akan lokaci ba.

Kara karanta wannan

Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa

Yan bindiga sun saki bidiyon 'yan mata 63 da suka sace a Katsina
Yan bindiga sun saki bidiyon 'yan mata 63 da suka sace a Katsina. Hoto: @HQNigerianArmy, Marrius Global View
Asali: Twitter

Yan matan na a cikin tawagar kai amaryar dakin mijinta a lokacin da 'yan bindigar suka sace su a ranar Alhamis a kauyen Gamji da ke Damari, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba a iya tantance lokacin da aka ɗauki bidiyon ba, amma dai ya fara yawo a shafukan sada zumunta a ranar Talata, inda aka ga masu garkuwan rike da makamai.

An kuma ga yadda ake suke dora bindigogi akan kafadar matan, ciki har da karamar yarinya sanye da hijabi mai ruwan omo.

Yan bindigan sun yi barazanar sake aurar da amarya

Wani daga cikin 'yan bindigar na sanye da kayan 'yan sanda yayin da wani kuma ke sanye da kakin sojoji.

"Zamu ga wanda ya isa ya karbe su ba tare da biyan kudin fansa ba. Gasu a nan, kuna kallon su, don haka ku daina yin karyar su 50 ne, kun dai gansu nan su 63 ne har da direba."

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

- Wani daga cikin 'yan bindigar yake fada a cikin bidiyon da harshen Hausa.

A hannu daya kuma bidiyon ya nuna jerin 'yan matan da aka yi garkuwa da su tare da wasu 'yan bindiga hudu tsaye a kansu.

"Wannan ita ce amaryar, za mu sake yi mata wani sabon aure idan har ba a biya kudin fansa ba. Wannan shi ne direban su."

- A cewar ɗan bindigar da ke rike da abin daukar bidiyon, kamar yadda aka ji muryarsa.

Matan da aka yi garkuwa da su, sun yi magana a bidiyon inda suka roki jama'a da su taimaka a biya kudin fansa don a sake su.

Kalli bidiyon a kasa:

Abin da iyaye da 'yan uwan amaryar ke cewa

Iyaye da 'yan uwan amaryar sun bayyana cewa 'yan bindiga sun nemi naira miliyan 100 kudin fansar dukkanin 'yan matan.

"Babu wanda ya taba rike irin wadannan makudan kudade da suka nema, mun fada masu gaskiya cewa bamu da kudin."

Kara karanta wannan

An gano gawar 'yar jami'ar Najeriya a dakin kwananta

- A cewar Haruna Abdullahi, wani dan uwan amaryar a zantawarsa da Premium Times a ranar Laraba.

Mazauna Katsina sun ba Dikko Radda shawarar mafita

Wasu daga cikin mazauna jihar Katsina, musamman daga shiyyar Funtua, sun koka kan yadda 'yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a jihar.

Nura Haruna Maikarfe, wanda mai fashin baki ne kan harkokin tsaro a shiyyar Funtua, ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa, an fara samun saukin matsalar tsaro a wasu garuruwan jihar.

Sai dai Haruna Maikarfe ya ce 'yan bindigar su ma sun dauki sabon salo tun bayan da Gwamna. Dikko Radda na jihar ya kaddamar da jami'an tsaro mallakin jihar.

A cewar sa:

"Sace wadannan 'yan matan na zuwa bayan da mai girma gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya kaddamar da dakarun tsaron jihar, wanda ke nuna maka cewa 'yan bindigar sun canja salo.
"A baya-bayan nan an samu hare-haren 'yan bindiga har ma wani sansanin soji, sannan an tare motocin matafiya an kashe na kashewa an sace wasu."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

Maikarfe ya yi kira ga gwamnan jihar da ya samar da kayan zamani irin su karamin jirgin leken asiri, kamarorin CCTV, hadin kai da kamfanonin sadarwa don gano mabuyar 'yan bindigar.

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjoji a hanyar su ta zuwa Abuja

A wani labarin kuma, wasu 'yan bindiga sun tare manyan motoci biyu a jihar Kogi da ke kan hanyar zuwa Abuja, kuma sun sace dukkan fasinjojin da ke ciki.

An ruwaito cewa, wani mutum da matarsa ta ke cikin fasinjojin ya yi magana da 'yan bindigar, inda suka nemi ya ba su naira miliyan 15 kudin fansar matarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel