Sojoji Sun Cafke Mace Mai Garkuwa da Mutane Yayin Karbar Kudin Fansa a Taraba

Sojoji Sun Cafke Mace Mai Garkuwa da Mutane Yayin Karbar Kudin Fansa a Taraba

  • Rundunar sojin Najeriya ta kama wata mata da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da haɗa baki da wasu
  • An tattaro cewa an kama matar ne a wurin karɓar kuɗin fansa bayan da shugaban ƙungiyarsu ya sanya ta karɓi kuɗin
  • Wani bincike da aka yi ya tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutanen yana auren mai karɓar kuɗin fansa da sojoji suka kama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun soji na bataliya ta 93 ta sojojin Najeriya sun kama wata mata da ake zargin tana da hannu wajen yin garkuwa da mutane.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an kama ta ne a lokacin da take ƙoƙarin karɓar kuɗin fansar wani da aka yi garkuwa da shi a Jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Katsina

Sojoji sun cafke mai garkuwa da mutane a Taraba
Sojoji sun cafke mai garkuwa da mutane a jihar Taraba Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Bugu da kari, sun tsare wani sanannen dillalin makamai da ke ba da makamai ga masu aikata laifuka, ba kawai a Taraba ba har ma a wasu yankuna na Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa matar da ake zargin, tana auren wani riƙaƙƙen mai laifi wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin sanannen ɗan ta'adda Hana Terwase, wanda aka kashe.

Kakakin rundunar, Laftanar Oni Olubodunde, ya ce an kama Janet Igohia, mai shekara 31 wacce da ake zargi da yin garkuwa da mutane ne bayan da ta karɓi Naira miliyan 1.5, kudin fansa na wani da aka yi garkuwa da shi a yankin Chanchangi na ƙaramar hukumar Takum a jihar.

Bayanin matar da ake zargi satar mutane ne

Kakakin ya bayyana cewa Igohia ta amsa cewa ta auri Voryor Gata, wani fitaccen mai aikata laifin da a baya ya riƙe mukamin mataimakin marigayi Gana Terwase.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin matsi a Najeriya, Remi Tinubu ta fadi lokacin da sauki zai zo

A kalamansa:

"A halin yanzu tana auren shugaban ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya a Kudancin Taraba. A cewarta, a baya ta auri wasu manyan masu aikata laifuka irin su marigayi Terkibi Gemaga wanda aka fi sani da Mopol, shahararren mai garkuwa da mutane da sojoji suka kashe shekaru biyar da suka gabata."

Laftanar Olubodunde ya kuma bayyana cewa sojojin da ke a Mararaba Baissa da ke karamar hukumar Donga sun kama wasu ƙarin mutane biyu da ake zargi da safarar bindigogi.

Hanyar Magance Rashin Tsaro a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana hanyar da za a bi domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya.

DHQ ta bayyana cewa dole ne ƴan Najeriya su sanya kishin ƙasarsu a zukatansu idan suna son a kawo ƙarshen matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel