Manyan Labarai A Yau
Alkalin kotun laifuka na musamman, Justis Oluwatoyin Taiwo, ya yankewa Bolarinwa Abiodun, wani janar din soja na bogi hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.
Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan Reverend Daniel Umaru na Cocin EYN da ke Njairi a karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa, inda suka kashe ‘ya’yansa maza.
Peter Obi ya sharara karya game da kwangilar Siemens. Hadimin shugaba Muhammadu Buhari ya zargi ‘dan takaran shugaban kasa da yi wa mutane karya kwanan nan.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da 'yan Boko Haram suka kai kan gidan gyara hali na Kuje.
An kara tsaurara matakan tsaro a garuruwan da ke yankin Kuje da kewaye a babbar birnin tarayya, Abuja bayan farmakin da yan Boko Haram suka kai kurkukun Kuje.
Matuka Keke Napep sun fadawa Bola Tinubu a takarda cewa babu wanda ya kamata ya dauka irin Buba Marwa, an nemi ayi na’am da takarar Tinubu-Marwa a zaben 2023.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa ya fi son matashi mai jini a jika ya zamo abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.
Bayan farmakin da wasu yan bindiga suka kai, fursunoni sama da guda 300 ne suka tsere daga babban gidan gyara hali na Kuje da ke babbar birnin tarayya Abuja.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Hajiya Saratu A. Umar a matsayin shugabar hukumar bunkasa jari ta Najeriya (NIPC) na tsawon shekaru biyar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari