‘Daga zuwa aikin gida na zama matar gida’, cewar wata budurwa yayin da ta wallafa bidiyonta

‘Daga zuwa aikin gida na zama matar gida’, cewar wata budurwa yayin da ta wallafa bidiyonta

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya yayin da ta yi murnar samun yanci daga mai aiki zuwa matar gida
  • Sabuwar amaryar wacce ta cika da farin ciki ta je dandalin TikTok don wallafa bidiyonta yayin da take taka rawa
  • Sai dai ta yi na’am da wani sharhi da wata tayi don kare ta cewa tun farko bata ambaci cewa ubangidan nata na da aure ba

Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan ta wallafa wani bidiyo a dandalin sadarwa ta TikTok dauke da rubutun, “daga mai aikin gida zuwa matar gida.”

A bidiyon da ta wallafa, an gano matashiyar matar dauke da murmushi a fuskarta yayin da take zaune a bayan mota tana rawar wata waka mai suna ‘Competition’ wato ‘gasa’ wanda Mayorkun ya rera.

Kara karanta wannan

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

Matashiyar budurwa tana rawa
‘Daga zuwa aikin gida na zama matar gida’, cewar wata budurwa yayin da ta wallafa bidiyonta Hoto: TikTok/@bomat_opeke
Asali: UGC

Wata mai amfani da shafin soshiyal midiya mai suna @confirmibadanbabe ta tambaya a bangaren sharhi,

“Da fatan ba mijin uwar dakinki kika aura ba dai.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Shine fa,” matar ta mayar da martani.

Shafin @lindaikejiblogofficial ta dauko hoton tambayar da amsar da ta bayar sannan ta wallafa shi a Instagram.

A wani yanayi mai ban mamaki, matar ta kuma yi na’am da sharhin da wata tayi tana mai kare ta.

Sharhin wanda wata mai suna @cinderella ademu ta yi ya ce:

“Ji mana amma ba ta ambata cewa yana da aure bah aka kuma bata ambata cewa ta auri wanda take yiwa aiki ba.”

Kalli bidiyon a kasa:

Ga bidiyo da martanin nata:

Mabiya shafin soshiyal midiya sun yi martani

@kolawokola123 ya ce:

"Mutanen Tik Tok sun iya karya amma idan ba karya bane...yar’uwa a’a. Ba komai za ku dunga yadawa ba fa.”

Kara karanta wannan

Asirin ‘Yan ta’adda ya tonu, Dakarun Sojoji sun bankado shirin hare-haren da za a kai

@coolkikismiles ta ce:

“Allah yasa mijin naki ya barki saboda taki ‘yar aikin."

@ice_10k_ ta ce:

"Kema haka wata yar aikin za ta karbe abun da kika karba daga yar’uwarki mace.”

Adam Zango ya saki zafafan hotunansa tare da amaryarsa yayin da suka cika shekaru 3 da aure

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu ne shahararren dan wasan nan na Hausa kuma mawakin zamani, Adam A. Zango ya cika shekaru da auren amaryarsa, Safiya Chalawa.

Adam Zango ya raya wannan rana ta musamman inda ya saki wasu zafafan hotunansa da matar tasa domin murnar wannan tafiya da ta fara mika a rayuwarsu.

Ana ganin wannan murna tasa ba zai rasa nasaba da yadda suka shafe tsawon shekaru uku ba tare da an ji kansu da amaryar tasa ba sakamakon lakabi da ake masa da mai yawan auri-saki.

Kara karanta wannan

Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko

Asali: Legit.ng

Online view pixel