Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

  • An yi arangama tsakanin mambobin kungiyar IPOB da wasu abokan hamayyarsu a a Ihiala da ke jihar Anambra
  • Karon da aka yi tsakanin kungiyoyin wadanda suka addabi yankin na kudu maso gabas ya yi sanadiyar halaka wasu mutane biyar
  • Kakakin yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce bai riga ya samu rahoto game da lamarin na Ihiala ba

Anambra - Jaridar Punch ta rahoto cewa an kashe mutane biyar Mutum b

Wani ganau da ya ga motar Hilux din da ke dauke da gawarwakin yan kungiyar daga garin ya ce mutane na ta jinjinawa yan IPOB din wadanda ke ta harbi a iska yayin da suka doshi hanyar babbar titin Onitsha-Owerri.

Taswirar jihar Anambra
Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra Hoto: Punch
Asali: UGC

Shaidan ya ce:

“Da gaske ne. Lamarin ya afku ne a kauyen Akwa da ke Ihiala lokacin wani karo tsakanin yan IPOB da wasu yan bindiga.

Kara karanta wannan

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yan bindigar suna da sansani a wani wuri da ake kira Oseakwa, daga inda suke ta addabar Ihiala, Okija, Uli da sauran garuruwan da ke makwabtaka.
“Tsawon wani lokaci yanzu, yan bindigar na ta addabar taron jana’iza sannan suna neman a fara ganinsu kafin a shirya kowani taro. Sune kuma suke ta garkuwa da mutane da kwace motoci.”

Kungiyar IPOB din ta hannun sakataren labaranta, Emma Powerful, ta sha nesanta kanta daga kashe-kashen da ke faruwa a Anambra da kudu maso gabas gaba daya, inda ta yi gargadi cewa za ta dauki mummunan mataki kan masu amfani da sunanta wajen aikata laifuka a yankin.

Daily Trust ta tattaro cewa wasu mutane da ake zaton yan Ebubeagu ne sun kara da yan bindiga a Ihiala a yayin wani taron jana’iza, sai dai ba a rasa rai ba.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Yan Najeriya basu damu da addinin yan takara ba – Baba Ahmed

Da yake martani kan lamarin, kakakin yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce bai riga ya samu rahoto game da lamarin na Ihiala ba.

Bayelsa: Fusatattun Matasa Sun Kona Wani Da Ake Zargi Da Sata

A wani labarin, wasu fusatattun matasa, a ranar Asabar sun kona wani da ake zargin barawo ne a Bayelsa, babban birnin jihar.

Lamarin ya faru ne a kusa da Customs Road Junction a Biogbolo-Epie kusa da babban titin Isaac Boro kamar yadda The Punch ta rahoto.

Wanda ake zargin, da ba a iya tabbatar da sunansa ba, an ce an kama shi ne wai yana sace wani waya mai tsada daga hannun wani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel