Jihar Neja: Yan gudun hijira sun koma gida don yin noma, suna tsoron sabbin hare-hare

Jihar Neja: Yan gudun hijira sun koma gida don yin noma, suna tsoron sabbin hare-hare

  • Yan gudun hijira musamman manoma a wasu kananan hukumomin jihar Neja sun fara komawa gidajensu
  • Sai dai kuma manoman na zaman dar-dar don gudun kada maharan su sake far masu musamman ganin cewa babu jami'an tsaro a yankunan
  • Yawancinsu sun baro matansu da yara a garin Minna, babbar birnin jihar domin su samu saukin guduwa koda za a sake kawo masu farmaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Yan gudun hijira daga kananan hukumomin Munya da Shiroro da ke jihar Neja sun fara komawa gidajensu cike da fargaba.

Daily Trust ta tattaro cewa yayin da zaman lafiya ya dawo sannan manoma suka fara komawa ga ayyukansu na noma, har yanzu mazauna yankin na cikin tsoro saboda rashin kasancewar jami’an tsaro a kasa.

Sun daura hakan ne a kan halin da suka shiga a baya inda yan bindiga suka dawo da mummunan horo bayan sun fara komawa gida yayin da gwamnati ta basu tabbacin samun ingantaccen tsaro.

Kara karanta wannan

An Kama Mafarauta 3 Kan Zargin Garkuwa Da Mutane a Adamawa

Taswirar jihar Neja
Jihar Neja: Yan gudun hijira sun koma gida don yin noma, suna tsoron sabbin hare-hare Hoto: Punch
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Idris Adamu, ya fada ma jaridar cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wasun mu sun koma gida don fara aiki kan gonakinmu saboda ba za mu iya rayuwa ba tare da noma ba. Amma yawancin wadanda ke komawa maza ne; wasu sun bar matayensu a garin Minna saboda za su samu saukin guduwa su kadai idan aka sake kawo farmaki.
“Ba wai cewa su (yan bindiga) sun daina bi ta garuruwan bane. Kwanaki hudu da suka wuce, an sace wani dan uwanmu a gonarsa lokacin da yan bindigar suke wucewa ta garin Kuchi. Sun karbe masa babur dinsa da wayarsa. An sake shi bayan kwana daya amma basu bashi babur da wayansa ba.”

Adamu, wani bakanikin babur, ya ce kauyawa na matukar shan wahala wajen rayuwa a birni saboda tsadar rayuwa.

Ya ce:

“Ina da mata da yara biyu yayin da matar kanina wanda yan bindiga suka kashe mijin nata ke zama da ni. Don haka nauyin ya yi mun yawa. Ba mu da zabin da ya wuce komawa gida.”

Kara karanta wannan

2023: Yadda limamin Katolika ya fatattaki yan cocinsa da basu da katin zabe

Adamu ya ce sun koma gida kawai sai suka tarar da an fasa wasu daga cikin dakunansu sannan aka sace kayayyaki.

Wani mazaunin yankin, Shehu Abubakar, ya ce hare-haren ya ragu har sai zuwa ranar Juma’a lokacin da yan bindiga suka sake kai farmaki Kuchi inda suka sace dabbobi mallakar wasu Fulani.

Legit.ng ta tuntubi wata yar gudun hijira mai suna Ya Mulango da ke samun mafaka a gidan yan uwansu da ke unguwar Maitunbi don jin ko suma suna shirin komawa gida inda tace:

“A’a babu zancen komawa gida a yanzu, rayuwa a birnin da wahala amma haka za mu ta lallabawa har lokacin da Allah zai kawo mana sauki.
“Bana fatan sake shiga tashin hankalin da muka shiga a baya saboda abu ne da ba zai taba gogewa a zukatanmu ba. Da farko ma bana iya bacci idan na rufe ido sai naga kamar yan bindigar za su sake kawo mana hari.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyensu Sanata Abba, sun halaka mutum 15, wasu sun bace

“Muna dai fatan komawa gida wata rana domin duk inda mutum zai kasance cikin walwala baya ga gidansa ne. Duk mun baro harkokinmu a chan.”

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi, a jihar Anambra.

An tattaro cewa an kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

An tattaro cewa an sace shugaban matasan ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni, lokacin da wasu yan bindiga suka farmaki gidansa da ke garin Ukpor.

Asali: Legit.ng

Online view pixel