2023: Budurwa ta rabu da saurayinta saboda baya goyon bayan Peter Obi ya gaje Buhari

2023: Budurwa ta rabu da saurayinta saboda baya goyon bayan Peter Obi ya gaje Buhari

  • Wata budurwa ta raba jaha da saurayinta saboda ya ki bin ra'ayinta na goyon bayan dan takarar shugaban kasa da take muradi a babban zaben 2023 mai zuwa
  • Budurwar mai suna Josephine ta bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi shine zabinta amma kuma saurayinta baya yin shi
  • Ta bayyana cewa babu yadda za a yi ta ci gaba da tarayya da mutumin da ba zai so abun da take so ba don haka ta ce kowa ya bi hanyarsa

Wata matashiyar budurwa mazauniyar birnin Abuja wacce aka ambata da suna Josephine ta rabu da saurayinta saboda ya ki goyon bayan dan takarar shugaban kasar da take so gabannin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa: Mata ta ta so na jika deliget da kudi, na ki, kuma na ci zabe

Josephine ta wallafa a shafinta na twitter cewa ita yar kashenin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ne.

Peter Obi da wata budurwa
2023: Budurwa ta rabu da saurayinta saboda baya goyon bayan Peter Obi ya gaje Buhari Hoto: PM News/Twitter/@JojoNitq
Asali: UGC

Da take bayyana masoyin nata a matsayin ‘wawa’, matashiyar ta ayyana cewa ba za ta iya ci gaba da soyayya da mutum kamar wannan ba musamman tunda ya ki bin sahun dan takarar shugaban kasa mafi soyuwa a wajenta.

Ta rubuta a shafin nata:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Don haka na kawo karshen soyayyarmu a yau saboda saurayina ya ki goyon bayan @PeterObi, ba zan iya ci gaba da soyayya da wawa ba.”

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan lamarin

@Gucho_milz ya yi martani:

“Ina goyon bayanki yar budurwa. Bai cancanci mallakar ki ba.”

@MatthewShamfe ya yi martani:

“Babu amfanin haka…kada mu tsani junanmu saboda zabinmu. Ki yi kokarin goyon baya da tallata dan takarar ki ga mutane amma idan basa ra’ayinsa…kada ki datse alaka da su…”

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

@boyowa_tobi ya ce:

“Kwantar da hankalinki.”

@demon6six6 ya ce:

"Saurayinki zai ci gaba da rayuwarsa.”

Mai kwadayi ya san gidan mai rowa: An taso fasto Mbaka a gaba bisa kiran dan takarar shugaban kasa marowaci

A wani labarin, shahararren limamin cocin Katolika, Ravaran, Father Ejike Mbaka na shan suka bayan kalaman da ya yi kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mbaka a yayin wani wa’azi ya bayyana Peter Obi a matsayin ‘matashi mai tsananin rowa’ inda ya bayyana cewa ba zai taba zama shugaban Najeriya ba.

A wani rahoto da Legit.ng Hausa ta buga a baya, Mbaka ya bayyana cewa Obi mutum ne da ba shi da karimci, inda ya kara da cewa bai kamata a amince dashi ya zama shugaban kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel