Yan majalisa na shirin tsige mataimakin gwamna bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yan majalisa na shirin tsige mataimakin gwamna bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

  • 'Yan majalisar dokokin jihar Oyo sun fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan
  • ‘Yan majalisar sun kaddamar da shirin ne a ranar Laraba, yayin zaman majalisar wanda kakakin majalisar, Adebo Ogundoyin ya jagoranta
  • Sun zargi mataimakin gwamnan da rashin da'a, cin mutuncin kujerarsa, almubazaranci da sauransu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rahotanni sun kawo cewa majalisar dokokin jihar Oyo ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.

A kwanan nan ne Olaniyan ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar Punch ta rahoto cewa bayan sauya shekar tasa, jam’iyya mai mulki a jihar ta bukaci ya yi murabus ko kuma a tsige shi.

Gwamna Makinde na jihar Oyo tare da mataimakinsa, Rauf Olaniyan
Da dumi-dumi: Yan majalisar dokokin Oyo na shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Hoto: Oyo State Government
Asali: Facebook

‘Yan majalisar jihar na jam’iyyar PDP ne suka sanya hannu a takardar. Mambobi 24 daga cikin 32 na majalisar sun sanya hannu kan korafin wanda Olaniyan ya karanto a zaman majalisar na ranar Laraba, 15 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Bayan sauya sheka zuwa APC, Kujerar mataimakin gwamnan PDP ta fara tangal-tangal, Majalisa zata tsige shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A takardar, an zargi mataimakin gwamnan da rashin da’a, cin mutuncin kujerarsa, almubazaranci da kudi, watsi da kujerarsa da kuma ayyukansa, rashin biyayya da sauran laifuka, TVC News ta rahoto.

‘Yan majalisar da suka rattaba hannu a kan takardar sun hada da: Fadeyi Muhammed (Ona Ara), Onaolapo Sanjo (Ogbomosho South), Babalola Olasunkanmi (Egbeda), Adebisi Yussuf (Ibadan Southwest 1), Okedoyin Julius (Saki West) da Adebayo Babajide (Ibadan North 2).

Sai kuma: Kehinde Olatunde ( Akinyele 2); Gbadamosi Saminu (Saki East/Atisbo), Mabaje Adekunle (Iddo), Oluwafowokanmi Oluwafemi (Ibadan Southwest 2), Akeem Adedibu (Iwajowa), Fatokun Ayo (Akinyele 1), Rasak Ademola (Ibadan South East 1), Obadara Akeem (Ibadan North West), Oyekunle Fola (Ibadan North 1), Adetunji Francis (Oluyole).

Sauran sune: Olajide Akintunde (Lagelu), Mustapha Akeem (Kajola), Popoola Ademola (Ibadan South East 2), Owolabi Olusola (Ibadan North East 2), Olagoke Olamide (Ibadan North East 1), Olayanji Kazeem (Irepo/Olorunsogo), Ojedokun Peter (Ibarapa North/Centre).

Kara karanta wannan

Babagana Kingibe ya aika sunayen mutum 3 ga Tinubu ya zabi abokin takara harda tsohuwar minista ciki

Magatakardar majalisar, Yetunde Awe ne ya karanta takardar.

Kakakin majalisar, Adebo Ogundoyin, ya ce korafin ya cika kaso biyu bisa uku da ake bukatar na fara shirin tsige shi.

Ya ce ‘yan majalisar za su bai wa mataimakin gwamnan wa’adin kwanaki bakwai domin ya mayar da martani kan zargin da ake masa. Kwanaki bakwan zai kare a ranar 22 ga watan Yuni.

Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A baya mun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Olaniyan ya sanar da sauya shekar tasa ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya ce ya yanke hukuncin ne saboda amsa kiran magoya bayansa wadanda suka gaji da jira bayan suna ta jiran tsammani a PDP na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel