Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna

Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna

  • Kimanin yan takara goma sha shida ne aka bayyana suna fafutukar neman kujera ta daya a Ekiti gabannin zaben gwamnan jihar da za a yi
  • Haka kuma ‘yan takarar na ta kamfen a jihar, inda suke bayyana shirinsu tare da yin kira ga jama’a da su zabe su
  • Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa zaben zai ba da sha'awa, idan aka yi la'akari da sahihanci da farin jinin 'yan takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti wanda zai samar da magajin gwamna mai ci, Dr Kayode Fayemi.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa kimanin yan takara takwas da doriya ne za su fafata a zaben.

Legit.ng ta tattaro sunaye da jam’iyyun siyasar wasu daga cikin yan takarar gabannin zaben na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwani: Yadda wasu 'Yan takaran APC suka kamu gaibu, suka sha kashi a hannun Bola Tinubu

1. Reuben Famuyibo (AP)

Dan takarar kujerar gwamna a zaben Ekiti
Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna Hoto: Reuben Famuyibo
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana daukar dan takarar gwamna na jam’iyyar Accord Party (AP) a zaben ranar 18 ga watan Yuni mai zuwa, Basorun Reuben Famuyibo (BRF), a matsayin daya daga cikin wadanda suka kafa jihar Ekiti.

Tsohon dan takarar kujerar shugaban kasar na 1993 mai shekaru 63 ya gina kansa a siyasar jihar da ma na kasar.

2. Moses Olajide (AAC)

Dan takarar kujerar gwamna a zaben Ekiti
Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna Hoto: Moses Olajide
Asali: Facebook

Jam’iyyar African Action Congress Party (AAC) ta zabi Revd. Ajagunigbala Moses Olajide a matsayin dan takararta a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka shirya yi a ranar 18 ga watan Yunin 2022.

Dan takarar na AAC ya bayyana cewa zai inganta cibiyoyin kiwon lafiya sannan ya sabonta tsarin sufuri a jihar idan aka zabe shi gwamna.

3. Oluwole Oluyede (ADC)

Dan takarar kujerar gwamna a zaben Ekiti
Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna Hoto: Oluwole Oluyede
Asali: Facebook

Likita haifaffen Ikere-Ekiti wanda ya zama dan siyasa ya kasance babban dan takara a zaben fidda gwani na APC a 2018 wanda gwamna mai ci ya lashe tikitin.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

Bayan ya gaza cimma kudirinsa a APC da kuma hukuncin da ya yanke na son kasancewa a takarar zaben na ranar 18 ga watan Yuni, sai kwararren likitan mai shekaru 57 ya fice daga jam’iyyar inda ya yada zango a jam’iyyar the African Democratic Congress (ADC), wacce a cikinta ya lashe tikitin takarar.

4. Kemi Elebute-Halle (ADP)

Yar takarar kujerar gwamna a zaben Ekiti
Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna Hoto: Kemi Elebute-Halle
Asali: Facebook

Yar takarar jam’iyyar African Democratic Party, Kemi Elebute-Halle, ta kasance daya daga cikin mata biyu da ke neman kujerar gwamna a zaben.

Injiniya kuma mai taimakon jama’ar mai shekaru 40, ta shafe tsawon shekaru tana aikin taimakawa mutane musamman marasa galihu a jihar.

A daidai lokacin da masu ruwa da tsaki ke neman karin mata a harkar siyasa, takararta ya samu gagarumin goyon baya daga wajen mata.

5. Abiodun Oyebanji (APC)

Dan takarar kujerar gwamna a zaben Ekiti
Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna Hoto: Abiodun Oyebanji
Asali: Facebook

Ko shakka babu Oyebanji mai shekaru 54 zai ba da wuta a zaben ranar 18 ga watan Yuni saboda wasu dalilai da dama da za su taimaka masa.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

Tsohon sakataren gwamnatin jihar ya samu damar aiki a karkashin gwamnoni biyu a jihar - Adeniyi Adebayo da Dr Fayemi.

6. Peter Adegbenro (APM)

Dan takarar kujerar gwamna a zaben Ekiti
Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna Hoto: Peter Adegbenro
Asali: Facebook

Adegbenro Fagbemi shahararren dan takarar gwamna ne a karkashin jam’iyyar Allied Peoples Movement a zaben gwamnan jihar Ekiti mai zuwa.

An san shi sosai kasancewar ya yi shugaban IPAC na jihar Oyo.

7. Olufemi Obidoyin (APGA)

8. Modupe Olatawura (APP)

9. Olugbenga Daramola (LP)

10. Oladosu Fatomilola (NNPP)

11. Ifedayo Iyaniwura (NRM)

12. Bisi Kolawole (PDP)

13. Olaniyi Agboola (PRP)

14. Olusegun Oni (SDP)

15. Adebowale Ajayi (YPP)

16. Kolade Akinyemi (ZLP)

Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, in ji wani malamin addini

A wani labarin, shugaban kungiyar kare hakkin Kirista da Musulmi, Prophet Iwu Jideogu Ogbu, ya bayyana wanda zai lashe babban zaben 2023 mai zuwa.

A cewar Ogbu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ne zai lashe babban zaben mai zuwa

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Kwankwaso ne zai daga tutar jam’iyyar NNPP wacce ta shafe shekaru sama da 20 amma ba’a jinta bayan ya farfado da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel