Bayan ya bar APC, Adamu Aliero ya lashe tikitin PDP na Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya

Bayan ya bar APC, Adamu Aliero ya lashe tikitin PDP na Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya

  • Tsohon gwamnan jihar Kebbi kuma Sanata mai wakiltan yankin Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, ya lashe tikitin jam’iyyar PDP
  • Aliero wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan, ya lallasa mamba na kwamitin amintattun jam’iyyar a zaben fidda gwanin
  • Tsohon gwamnan ya samu kuri’u 246 wajen yin nasara yayin da Alhaji Haruna Saidu ya samu kuri’u 16

Kebbi - An zabi Sanata Mohammed Adamu Aliero a matsayin dan takarar kujerar Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ya kayar da babban abokin karawarsa, Alhaji Haruna Saidu, na kwamitin amintattu na jam’iyyar da kuri’u 246 inda shi kuma ya samu 16, jaridar Leadership ta rahoto.

Sanata Adamu Aliero
Bayan ya bar APC, Adamu Aliero ya lashe tikitin PDP na Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya Hoto: @bbchausa.
Asali: Twitter

Aliero wanda ya kasance tsohon gwamnan na jihar Kebbi tsakanin 1999 zuwa 2007 shine ke kan kujerar sanata mai wakiltan yankin Kebbi ta tsakiya a yanzu haka.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

A sakonsa na godiya, Aliero ya nuna godiyarsa ga deliget da magoya bayansa a fadin jihar, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan lashe tikitin, Aliero ya yi alkawarin dandanawa al’ummar mazabarsa romon dimokradiyya.

Ya yi kira ga magoya bayan PDP da su zabi sahihan yan takara a babban zaben kasar mai zuwa idan har suna son APC ta bar mulki.

Kimanin yan majalisar dokokin tarayya da na jiha 18 ne suka sauya sheka tare da Aliero zuwa PDP.

Adamu Aliero, Dakingari Da Wasu Jiga-Jigan APC a Kebbi Sama Da 30 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

A baya mun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Kebbi Adamu Aliero da wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress, APC a Jihar Kebbi sun fita daga APC sun koma PDP.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

BBC Hausa ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya ce rashin adalci da aka yi yayin zaben fidda gwani a Kebbi na daga cikin abubuwan da yasa suka fice daga APCn.

Aliero, wanda ya taba yin gwamna a Kebbi har sau biyu da kuma tsohon minista a Abuja ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar yana mai jadada rashin jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da harkokin jam'iyyar ta APC a Kebbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel