Yadda wasu ma’aikatan gidan gona a Abuja suka kashe ubangidansu, suka jefa gawarsa a cikin rijiya

Yadda wasu ma’aikatan gidan gona a Abuja suka kashe ubangidansu, suka jefa gawarsa a cikin rijiya

  • Wasu ma’aikatan gidan gona da ke yankin Kuje na babban birnin tarayya sun kashe ubangidansu.
  • Ma’aikatan da ke aiki karkashin matashin mai suna Aliyu Takuma sun kashe shi sannan suka jefa gawarsa a cikin rijiya da ke kusa da gonarsa
  • Hakazalika, makasan nashi sun kuma sace wasu daga cikin dabbobin mamacin da suka hada da tumakai da shanaye 40

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rundunar yan sanda a Abuja sun bayyana yadda ma’aikata da ke aiki karkashin wani manomi mai suna Hussaini Aliyu Takuma suka kashe shi sannan suka jefar da gawarsa cikin wata rijiya da ke kallon gonarsa.

Lamarin ya afku ne a garin Jeida da ke yankin Kuje na babban birnin tarayya Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yadda wasu ma’aikatan gidan gona a Abuja suka kashe ubangidansu, suka jefa gawarsa a cikin rijiya Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa manomin ya bata daga gonarsa tun a ranar 2 ga watan Yuni, amma bayan an gudanar da bincike da kyau, sai aka gano cewa an kashe shi ne sannan aka jefa gawarsa a rijiya.

Kara karanta wannan

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

Sahara Reporters ta rahoto cewa hedkwatar yan sandan Kuje a ranar Asabar, ta ciro gawar Hussaini daga rijiyar, inda aka dauke shi zuwa babban asibitin gwamnati na Kuje domin bincike.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take tabbatar da lamarin, mataimakiyar kakakin yan sandan babban birnin tarayya, Oduniyi Omotayo, ya bayyana cewa yan sandan yankin Kabusa da ke Abuja sun kama makasan yayin da suke hanyarsu ta zuwa Kano da dabbobin da suka sace mallakin marigayin.

Omotayo ta kuma bayyana cewa ana kan gudnar da bincike kan lamarin kuma za a sanar da jama’a sakamakon binciken a kan lokaci.

Ta ce:

“Dan uwan marigayin ne ya kai rahoton lamarin hedkwatar yan sanda ta Kuje a ranar 4 ga watan Yunin 2022, cewa dan uwansa ya bar gida a ranar 2 ga watan Yuni, 2022, zuwa gonarsa amma bai dawo ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

“Yan sanda sun shiga aiki, inda suka shiga bincike kan lamarin, an kama mutum biyu da suke aiki a gonar marigayin a yankin Kabusa yayin da suke hanyarsu ta zuwa Kano da dabbobin da suka sata mallakin marigayi ubangidan nasu.”

Kakakin yan sandar ta kara da cewar bayanan da suka samu daga wadanda suka kashe mutumin ya kai ga gano gawar Takuma a cikin rijiyar.

Majiyoyi sun bayyana cewa kimanin tumakai 40 da akuyoyi shida ma’aikatan gonar suka sace bayan sun kashe ubangidan nasu.

Yan bindiga sun sace wani malamin addini da matarsa, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansa

A wani labarin kuma, tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da Limamin cocin Anglican na Jebba da ke jihar Kwara, Rt. Rev. Aderogba, matarsa da kuma direbansa a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni a babbar hanyar Oyo/Ogbomoso.

Jaridar Punch ta rahpoto cewa malamin addinin da matarsa na hanyarsu ta zuwa jihar Kwara ne lokacin da motarsu ta baci a wani wuri da babu mutane da misalin karfe 8:30 na dare.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Ba a jima ba sai ga yan bindigar sun farmake su sannan suka tisa keyarsu zuwa cikin jeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel