Malaman addini: Ku dai bi hukuncin da kotu ta yanke kan dokar sanya hijabi

Malaman addini: Ku dai bi hukuncin da kotu ta yanke kan dokar sanya hijabi

  • Kungiyar malamai ta NATAIS ta yi martani a kan batun saka hijabi zuwa makarantun Boko musamman jihohin kudancin kasar
  • NATAIS ta bukaci makarantu a fadin kasar da su mutunta hukuncin kotun koli da ya baiwa dalibai mata damar saka hijabi
  • Ta kuma koka a kan furucin wasu kungiyoyin addini wanda a cewarsa zai zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban kasar

Osun - Kungiyar malaman koyon Larabci da addinin Islama na Najeriya (NATAIS) ta bukaci makarantu a fadin kasar da su mutunta hukuncin kotun koli kan amfani da hijabi a makarantu.

A ranar 17 ga watan Yuli ne kotun koli ta amincewa dalibai mata su dunga sanya hijabi zuwa makarantu a jihar Lagas.

Kotun ta yi watsi da karar da gwamnatin jihar Lagas ta daukaka sannan ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke cewa haramta hijabi cin zarafi ne a kan dalibai musulmai a jihar.

Kara karanta wannan

Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na

Yaran makaranta
Malaman addini: Ku dai bi hukuncin da kotu ta yanke kan dokar sanya hijabi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

NATAIS, a wata takarda da ta fitar bayan taronta na kasa a jami’ar Fountain da ke Osogbo, jihar Osun, ta bukaci hukumomin makaranta da su mutunta yancin dalibai mata Musulmai wadanda suka zabi sanya hijabi a makarantu, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takardar na dauke da sa hannun Farfesa Musa Adesina Abdu-Raheem, shugaban kungiyar da kuma sakataren kungiyar Dr Muhammad Shariff Ramadan.

Malaman sun kuma nuna damuwa cewa furucin wasu kungiyoyin addinai a kasar na barazana ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Jaridar ta kuma rahoto cewa malaman sun nuna damuwa a kan watsi da batun daukar malaman Larabci da na Islama a makarantun firamare da sakandare musamman a jihohin kudu maso yamma.

Sun bukaci gwamnati a dukkan matakai da su kwashi malaman koyon Larabci da addinin Islama don koyar da matasa yan Najeriya addini da ilimin tarbiya, cewa hakan zai rage fashi da Kakakin, cin hanci da rashawa da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan Ta'addan Ansaru Sun Kwace Wasu Yankuna, Sun Haramta Harkokin Siyasa

Sun bukaci gwamnati da ta jajirce don kawo karshen rashin tsaro.

Bayan Halasta Saka Hijabi, Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Tafi Kotun Koli Sanye Da Tufafin Bokaye

A wani labarin kuma, mun ji cewa lauya mai kare hakkin bil adama, Malcolm Omoirhobo, a ranar Alhamis, a ranar Alhamis ya kwashi yan kallo saboda irin tufafin da ya saka yayin zuwa kotun koli a Abuja, rahoton The Punch.

Hotunan da aka yada a dandalin sada zumunta sun nuna Omoirhobo sanya da tufafin lauya hade da wasu abubuwa da suka yi kama da na masu maganin gargajiya ko bokaye.

Lauyan ya saka sarka ta 'cowries' a wuyansa da fuka-fiki a kansa da wasu abubuwa a kafansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel