Da Ɗumi-Ɗumi: An shiga ruɗani kan batun Murabus ɗin CJN Tanko Muhammad

Da Ɗumi-Ɗumi: An shiga ruɗani kan batun Murabus ɗin CJN Tanko Muhammad

  • Duk da yaɗuwar rahoton murabus ɗin shugaban alkalan Najeriya, har yanzun hukumomin shari'a ba su ce komai ba kan batun
  • Wani Jami'ai a ofishin CJN ya tabbatar da cewa Tanko Muhammed ya je Ofis da safe, amma ya bar wurin ba zato ba tsammani
  • Ruɗani da rashin tabbas ya dabaibaye harkokin shari'a da suka shafi Ofishin shugaban Alƙalai tun bayan fitar rahoton murabus

Abuja - An shiga ruɗani da rashin makama kan harkokin sashin shari'a masu alaƙa da ofishin shugaban alƙalan Najeriya (CJN), kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Yayin da rahotanni ke yawo cewa Alkalin Alkalai na ƙasa, CJN Tanko Muhammad, ya miƙa takardar murabus daga kan mukaminsa, hukumomin shari'a sun ƙi cewa komai kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa yin wasu muhimman abubuwa

CJN Tanko Muhammad.
Da Ɗumi-Ɗumi: An shiga ruɗani kan batun Murabus ɗin CJN Tanko Muhammad Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Har yanzu, Kotun Ƙoli, hukumar kula da harkokin shari'a ta tarayya (FJSC) da hukumar (NJC) sun yi gum sun ƙi tabbatar da rahoto ko kuma akasin haka.

Mai magana da yawun CJN, Ahuraka Yusuf, Daraktan watsa labarai na Kotun Ƙoli, Festus Akande, da takwaransa na hukumar NJC ta ƙasa, Soji Oye, sun bayyana cewa ba zasu iya tabbatar da cigaban ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ko me ke faruwa a Ofishin CJN?

Wani bincike ya nuna cewa shugaban Alkalai na ƙasa, Tanko Muhammed, ya je Ofis ɗinsa da safiyar Litinin ɗin nan, amma ya bar ofishin mintuna kaɗan bayan zuwansa.

"Bamu san ainhin yanayin da harkokin shari'a (da suka shafi ofishin CJN) suka shiga ba yanzun. Mun ji raɗe-raɗin da ke yawo cewa CJN ya aje aiki, amma babu wanda ya ce komai kan lamarin."

Kara karanta wannan

Ga dukkan alamu APC, Tinubu sun shiga ruɗani, basu shirya wa zaɓen 2023 ba, Mataimakin Atiku

"CJN ya zo Ofis yau da sassafe amma bai jima ba, ba zato ya bar ofis. An gaya mun cewa yau be zo tare da tawagar da ya saba zuwa da ita ba."

- Inji wani Jami'i a Ofishin CJN

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin gwamnoni huɗu da suka ɗauki sabbin tsauraran matakan kawo karshen yan bindiga a jihohin su

Gwamnoni a Najeriya na cigaba da ɗaukar tsauraran matakan yaki da nufin dakile matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a jihohin su .

Yan ta'adda, yan fashin daji, yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran kashe-kashen masu aikata muggan laifuka na cigaba da hana zaman lafiya a wasu sassan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel